‘Yan sanda a Katsina sun daƙile yunƙurin kai hari a hanyar Sabuwa zuwa Kaya

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Bayani ya nuna cewa ‘yan bindigan sun tare matafiya a babban hanyar a ƙauyen Liman da ke ƙaramar hukumar Sabuwa.

Jami’an tsaron sun samu nasarar ƙubutar da mutanen da yan bindigan su kai garkuwa da su.

Kamar yadda bayani ya nuna jami’an tsaron sun yi wa ƙauyen Liman ƙawanya a yayin da suke gudanar da binciken gano yan ta’addan da suka aikata wannan ɓarna da maido da zaman lafiya a yankin.

By ukarofi