Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirinta na kafa cibiyar iskar gas (CNG) a kan hanyar Funtua–Gusau cikin garin Funtua a jihar Katsina, a wani ɓangare na ƙoƙarin faɗaɗa hanyoyin samar da makamashi mai tsafta da kuma inganta harkokin sufuri mai ɗorewa a Arewacin Najeriya.
Shugaban hukumar shirin shugaban ƙasa kan CNG da motoci masu amfani da lantarki, Presidential Initiative on CNG and EVs (PiCNG & EVs), Barrista Ismaeel Ahmad, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar girmamawa da tawagarsa ta kai wa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, a gidan gwamnatin Jihar Katsina.
An tsara wannan cibiyar domin samar da tankuna iskar CNG, cajin motocin lantarki, da kuma sauya motocin man fetur zuwa CNG, musamman ga masu harkokin sufuri na kasuwanci da masu zaman kansu da ke amfani da wannan muhimmiyar hanya da ke haɗa jihohin Katsina, Zamfara da sauran jihohin maƙwabta.
A nashi ɓangaren, Gwamnan Raɗɗa ya jaddada kudirin gwamnatinsa na goyon bayan wannan shiri, yana mai cewa hadin gwiwar ya dace da manufofin jihar na bunƙasa sufuri mai araha da kuma amfani da makamashi mai tsafta. Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta bayar da cikakken goyon baya domin ganin an aiwatar da shirin cikin nasara.
Domin tabbatar da fara aikin, Gwamnan ya umarci tawagar PiCNG da su gabatar da cikakken buƙatar fili da ake buƙata, tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ɗauki mataki cikin gaggawa bayan karɓar wannan buƙata.
Haka zalika, ya kuma bayyana irin ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi wajen inganta harkokin sufuri, ciki har da sayen manyan motocin guda 30 na alfarma da na zirga-zirga, inda aka riga aka sauya wasu daga cikinsu zuwa masu amfani da CNG ta hanyar haɗin gwiwa da kamfanin Greenville. Haka kuma, jihar ta fara amfani da motocin haɗaka (lantarki da dizal) a matsayin wani ɓangare na canja fasalin sufuri a fadin jihar da duniya baki ɗaya.
Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa gwamnatinsa tana cikin shirin sayen babura masu amfani da lantarki guda 3,000 domin malamai a karkara, tare da karin keken napep na lantarki guda 1,500, domin rage tsadar sufuri da kuma samar da damar bunƙasa tattalin arziki ga al’umma.
A nasa ɓangaren, Barrista Ismaeel Ahmad ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a fara kafa cibiyoyin sauya motocin man fetur zuwa CNG a jihar, tare da horas da matasa kimanin 500 a matsayin ƙwararrun masu gyara da kula da motocin CNG.
Mambobin tawagar sun haɗa da babban jami’in kula da bin ƙa’idoji, Injiniya Zayyan Tambari; Mataimakiyar Darakta kuma mai bai wa shugaban shirin shawara, Hadiza Lawal; Mai kula da wayar da kan alumma a kan CNG na yankin Arewa maso Yamma, Kwamared Jamilu Mikail da Babban Hafsan Ofishi, Tan Mayor Bright, da sauransu.
Wannan shiri na nuna ƙudurin Gwamnatin Tarayya da jihar Katsina na bunƙasa amfani da makamashi mai tsafta, ƙarfafa ƙwarewar cikin gida, da kuma haɓaka ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa a yankin da ma faɗin Nijeriya.
