Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano
Shugaban Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) na Jihar Kano, Hon. Haruna Musa Ungoggo, ya bayyana cewa sun gayyaci Sanata Rabiu Musa Kwankwaso domin ya shiga jam’iyyar, ganin cewa ya dace da manufofinta kuma jagora ne mai kawo nasara.
Ya bayyana hakan ne a wata ganawa da manema labarai, inda ya ce Kwankwaso na da kwarewa da hangen nesa a fannonin tsaro, ilimi, noma da sauran bangarori na ci gaban al’umma.
A cewarsa,
“Kwankwaso jagora ne da ke kawo nasara a kowace jam’iyya. ADC ma tamkar gidansa ne, domin manufofinsa sun yi daidai da na jam’iyyar.”
Ya ƙara da cewa sun miƙa masa jagoranci ne domin su samu nasara a zaɓen 2027 a dukkan matakai da yardar Allah.
Dangane da halin da ƙasa ke ciki, musamman a Arewa, Ungoggo ya ce ADC na da shirin kawo sauyi mai ma’ana.
“Idan aka duba halin da ake ciki a Nijeriya, musamman Arewa da ke dogaro da noma, kiwo da kasuwanci, za a ga cewa ADC ita ce mafita. Abin mamaki ma shi ne idan aka samu wanda zai zaɓi wata jam’iyya ba ADC ba,” inji shi.
Ya kuma bayyana cewa jiga-jigan ‘yan siyasa da dama na shirin komawa ADC, ciki har da Kwankwaso da Gawuna.
A ƙarshe, ya yaba wa ‘yan jam’iyyar ADC bisa gagarumar tarbar da suka yi wa Sheikh Ibrahim Khalil, ɗan takarar jam’iyyar a zaɓen 2023, a wani taro da aka gudanar a Kano.
