Kabiru Gusau ya zama shugaban jam’iyyar ADC a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau

Jam’iyyar African Democratic Congress ADC a Jihar Zamfara ta zaɓi sabin shugabannin ta na Jiha ta hanyar yarjejeniya da sasanci, inda Alhaji Kabiru Garba Gusau ya zama shugaban jam’iyyar na jiha.

An gudanar da taron amincewa a yau Litinin a babban masaukin baƙi watau Command Guest in dake a Gusau.

Sauran manyan shugabanin da aka zaɓa sun haɗa da, Kabiru Aliyu Bakura mataimakin shugaban jam’iyya, Sanusi Falalu, sakatare, Abdullahi Dahiru Odita, Ganiya Sani shugabar mata da Abdulkarim Umar a matsayin sakataren yaɗa labarai da sauransu.

A jawabinsa na amincewa, sabon shugaban jam’iyya, Kabiru Garba Gusau, ya nuna godiyarsa ga wakilai da dattawan jam’iyyar saboda amincewar da aka yi masa.

Shugaban ya ce an amince da zaɓen don inganta haɗin kai, rage rikicin cikin gida, da kuma sanya ADC don shiga cikin harkokin siyasa kafin babban zaɓen 2027.

Ya yi alƙawarin gudanar da gwamnati mai adalci da kuma haɗa kan jama’a wadda za ta mayar da Jam’iyyar ta ADC a matsayin mai ƙarfin gaske a siyasance a Jihar ta Zamfara.

“Ƙofofinmu a buɗe suke ga duk masu ra’ayin ci gaba waɗanda suka yi imani da siyasa mai tushe da kuma ci gaban jihar Zamfara,” in ji Gusau.

A cewarsa, jam’iyyar ADC tana ƙara himma wajen ƙarfafa kasancewarta a Zamfara a yayin da ake ci gaba da daidaita siyasa kafin zaɓen 2027.

Gusau, ya bayyana tsarin amincewa a matsayin wata alama ta ciyar da jam’iyyar a gaba a siyasance tsakanin ‘yan jam’iyyar ADC a jihar.

A cewarsa, sabbin Shugabannin za su ba da fifiko ga wayar da kan jama’a game da haɗa kan matasa da mata, da kuma kamfen ɗin da aka tsara bisa manufofin nasara a zaɓen da ke tafe.

Ya kuma yi kira ga ‘yan jam’iyyar da suke hangen ba a yi masu daidai ba da su dawo ayi tafiya tare a jam’iyyar, yana mai tabbatar musu da adalci da daidaiton damammaki a siyasance.

By ukarofi