
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
‘Yan Nijeriya mazauna Afirka ta Kudu sun koka game da abin da suka kira da sakaci daga ɓangaren Gwamnatin Tarayya akan abin da ya shafi lamuransu tare kira a gare ta da ta ɗauki matakan kare rayukansu da dukiyoyinsu sakamakon ƙarin zanga-zangar ƙin baƙi da ke ƙara ta’azzara a ƙasar.
Hukumar kula da lamuran ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje NiDCOM, ta bada umarnin rufe shaguna na ɗan lokaci tare da shawartar mutane su zauna a gidajensu na ɗan lokaci sakamakon fargabar ɓarkewar tashin-tashina.
An ruwaito cewa, wata zanga-zangada aka fara ta rikiɗa zuwa tashin hankali a wasu birane, inda aka samu lalata dukiyoyi da kuma jikkata mutane. Haka kuma akwai hasashen ci gaba da zanga-zanga a wasu yankuna na ƙasar.
Shugaban ƙungiyar NICASA, Rev. Frank Onyekwelu, ya bayyana damuwa kan abin da ke faruwa, inda ya buƙaci a gaggauta tattaunawa tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu domin kare haƙƙin ‘yan Nijeriya da sauran ‘yan ƙasashen Afirka.
Ya kuma yi kira da a samar da hanyoyin rahoto da bincike kan hare-haren ƙin baƙi, tare da ɗaukar mataki kan duk jami’an tsaro da aka samu da laifi.
A wata sanarwa da NiDCOM ta fitar da jami’in hulɗa da jama’arta, Abdur-Rahman Balogun, hukumar ta ce bayanan sirri sun nuna cewa an shirya gudanar da zanga-zanga a yankin Gauteng a tsakanin ranakun 27 da 29 ga Afrilu, 2026, domin matsi ga gwamnatin Afirka ta Kudu akan yawaitar baƙin haure acikin ƙasar.
