Majalisar Kano ta amince da Murtala Garo a matsayin mataimakin gwamna

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Majalisar dokokin jihar Kano ta amincewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamnan Kano.

Idan za’a iya tunawa a makon da ya gabata ne gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya miƙa wa majalisar sunan Murtala Sule Garo domin tantance shi ta kuma amince masa ya naɗa shi a kujerar mataimakin gwamnan Kano .

A ranar 27 ga watan mayu, 2026 ne dai tsohon mataimakin gwamnan Kano Aminu Abdussalam Gwarzo ya ajiye muƙaminsa bayan wata rashin jituwa da suka samu da Gwamna saboda ya gaza binsa zuwa jam’iyyar APC da ya koma.

Kazalika, majalisar dokokin ta Kano dai ta amince da Murtala ne bayan da kwamitin da ta naɗa ƙarƙashin jagoranci mataimakin shugaban majalisar Hon. Muhammad Bello Butu-butu ya gabatar da rahotonsa.

Kwamitin tantancewa na Majalisar Dokokin Jihar Kano ya bayyana cewa ya yi cikakken nazari kan takardun karatun Murtala Garo, ƙwarewarsa a aiki da kuma tarihin rayuwarsa, bisa tsarin tantancewar da majalisar ke bi.

Bayan tattaunawa kan rahoton kwamitin, ‘yan majalisar sun amince baki ɗaya da shawarwarin da aka gabatar, inda suka tabbatar da Garo a matsayin wanda ya cancanta kuma ya dace ya zama mataimakin gwamnan Jihar Kano.

Daga nan ne Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Ismail Falgore, ya sanar da amincewar majalisar, lamarin da ya baiwa Gwamna Abba Kabir Yusuf dama domin rantsar da Garo a matsayin sabon mataimakin gwamna.

By ukarofi