Kada ku yi wa sulhu da ƴan bindigar Katsina zagon-ƙasa – Sheikh Gumi ga hukumomin tsaro

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sanannen malamin addinin Islama a Nijeriya, Sheikh Ahmad Gumi ya yi gargaɗi game da yunƙurin yin zagon-ƙasa ga zaman sulhu da ake yi tsakanin ƙananan hukumomin jihar Katsina da jagororin ƴan bindiga.

Rahotanni sun bayyana cewa, malamin, wanda ke da fahimtar hanyar yin sulhu da ƴan bindiga ita ce mafita wajen kawo ƙarshen ayyukan ta’addancinsu ga al’umma, ya bayyana haka ne yayin da ake cigaba da samun nasara a zaman sulhu da ake yi da su a ƴan kwanakin nan a garuruwa daban-daban.

A ranar Asabar, 13 ga Satumba an ga yadda jagororin ƴan bindiga a Ƙananan Hukumomin Matazu da Faskari suka shiga zaman tattaunawa da al’ummar yankunan da nufin kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane a yankunan.

Da yake magana akan irin haka a Ƙaramar Hukumar Sabuwa, Sheikh Gumi ta kafar Facebook ya kirayi hukumomin tsaro da jagororin al’umma da kada su ci amana ko saɓa alƙawarin da aka ɗauka da su a yayin sulhun.

Ya kuma nemi gwamnati da ta mu’amalanci ƴan bindiga na arewa ta irin salon da aka yi amfani da shi wajen shawo kan matsalar mayaƙan yankin Neja-Delta.

Saidai a wani ɓangare kuma, tsohon Sanata kuma mai fafutukar ƴancin ɗan-adam, Shehu Sani ya soki shirin yarjejeniyar zaman lafiyar da ake yi, inda ya ce ya zama wajibi a gurfanar da ƴan bindiga domin su fuskanci hukuncin doka.

Kamar yadda ya sha wallafawa a kafafen sada zumunta, tsohon sanatan ya bayyana cewa gwamnatin tarayya da na jihohi suna sake maimaita hanyoyin da aka bi a baya waɗanda ba su yi ƙarko ba kuma babu wani sakamako mai ɗorewa da aka samu akan haka.

By Babaji