Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Babbar kotun tarayya da ke zama a birnin Abuja ta amince da ɗage ranar yanke hukunci na ƙarshe dangane da ƙarar da hukumar yaƙi da yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annati (EFCC) ta shigar, tana neman a ba ta damar ƙwace wasu manyan ƙadarori guda hamsin da bakwai (57) na tsohon ministan shari’a kuma babban lauyan ƙasa (AGF), Abubakar Chika Malami (SAN).
Alƙalin kotun, mai shari’a Emeka Nwite, ne ya sanar da ɗage zaman bayan da lauyoyin ɓangarorin biyu suka kammala gabatar da hujjojinsu na ƙarshe a gaban kotun.
Hukumar EFCC tana neman babban hukunci na dindindin (final forfeiture) kan waɗannan ƙadarori, waɗanda suka haɗa da manyan gidajen alfarma, otal-otal, da filaye da ke birnin Abuja, Kano, da jihar Kebbi, bayan da ta zargi cewa tsohon ministan ya mallake su ne ta hanyar amfani da kuɗaɗen haram da kuma karkatar da dukiyar ƙasa a lokacin da yake kan kujerar ministan shari’a a gwamantin Muhammadu Buhari.
A nasa ɓangaren, Abubakar Malami ta hanyar babban lauyansa, Mista Wahab Shittu (SAN), ya musanta dukkannin waɗannan zarge-zargen na EFCC baki ɗaya. Lauyan ya gabatar da takardun kariya inda ya bayyana cewa yawancin waɗannan ƙadarori an same su ne ta hanyar halal kafin da kuma lokacin da Malami yake riƙe da madafun iko, kuma matakin na EFCC ya saɓa wa ƙa’idojin shari’a.
Kotun ba ta sanar da takaimaiman sabuwar ranar da za ta dawo domin yanke hukuncin ba, sai dai ta bayyana cewa za a sanar da lauyoyin ɓangarorin biyu ta hanyar rubutacciyar wasiƙa nan ba da jimawa ba.
