Kaduna: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mutum shida yayin sallar asham a Kachia

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da masallata guda shida yayin da ake tsaka da gudanar da sallolin Tarawihi a wani masallaci da ke ƙauyen Azara a Ƙaramar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna.

Wani mazaunin yankin Azara mai suna Malam Tanimu Ibrahim, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Alhamis wayewar Juma’a yayin da al’umma ke tsaka da ibadar watan Ramadan.

A cewarsa, ’yan bindigar sun kutsa cikin ƙauyen inda suka fara harbe-harbe a iska domin tayar da hankalin jama’a, kafin daga bisani su shiga masallacin tare da yin awon gaba da mutane shida da suka ƙunshi maza huɗu da mata biyu.

Harin ya jefa al’ummar yankin cikin firgici da tashin hankali musamman ganin cewa an kai harin ne a cikin masallaci yayin gudanar da ibada a wata mai alfarma.

Wani jagora a ƙauyen da ya nemi a sakaye sunansa ya tabbatar da harin da kuma bayyana sunayen waɗanda aka sace kamar haka Saifullahi Harisu, Yakubu Yunusa, Abba Minkailu, Yusha’u Sadiku, Maryam Abdullahi da kuma Aisha Yakubu.

Ya ce, da safiyar Juma’a ‘yan bindigarsun kira ‘yan ƙauyen inda suka nemi a biya su Naira miliyan 30 a matsayin kuɗin fansa.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a samu cikakken bayani daga jami’an tsaro ba kan matakin da suka ɗauka dangane da lamarin. Sai dai mazauna yankin na kira ga hukumomi da su ƙara tsaurara matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a, musamman a wannan wata na azumi.

By Babaji