Iyalan El-Rufa’i sun magantu kan ikirarin ICPC na gano na’urorin naɗar murya a gidansa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Iyalan gidan tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, sun musanta rahotannin cewa an gano na’urorin naɗar murya a gidansa yayin bincike da jami’an Hukumar Yaƙi da Rashawa (ICPC) suka gudanar a Abuja.

A wata sanarwa da suka fitar a jiya Litinin da ke ɗauke da sanya hannun ɗansa Mohammed Bello El-Rufa’i, iyalan sun kuma nemi da a gurfanar da El-Rufa’in a kotu matuƙar akwai ababen da ake tuhumar sa a kansu.

Hakan na zuwa ne bayan da ICPC ta yi ikirarin cewa ta ƙwato wasu kayayyakin laturoni da ake zargin na naɗar murya ne da wasu muhimman takardun bayanan lamuran tsaro a gidan.

Hukumar ta bayyana haka ne a wata takardar ƙorafi da ta shigar wa Babbar Kotun Birnin Tarayya Abuja da ke bayar da amsa ga zargin El-Rufa’i na ikirarin an tauye masa ‘yanci.

Saidai, iyalan na El-Rufa’i sun bayyana cewa wannan ikirarin zallar wasan kwaikwayo ne da kuma yunƙurin haddasa cece-kuce acikin al’umma.

A cewarsu, abin da ICPC suka samo a gidan sune “tsofaffin wayoyin hannu da aka daina amfani da su, wasu sun jima har tsawon shekaru 20, sai kuma na’urorin ‘flash’ da ‘laptops’.”

Sun kuma zargi hukumar da amfani da shurun El-Rufa’i wajen matsa masa lamba, inda suka yi gargaɗin cewa kowane ɗan ƙasa yana da ‘yancin yin shuru yayin bincike, wanda hakan ba shi ke nuna ya ƙi bayar da haɗin kai ba.

Kazalika, sun ƙalubalanci sahihancin ayyukan ICPC da cin alwashin ganin an kammala shari’ar bisa gaskiya da adalci.

By Babaji