Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Gaskiyar magana sai dai ɗan ta’adda ko mai zuga tada fitina ya fake da wani addini ko ƙabila don samun mafaka ko dalilin aikata mugun aikinsa. Ba yadda za a yi mai yin sallah da gaskiya ya zama ɗan ta’adda sai dai gafalalle ko munafuki. Kazalika ba mabiyin addinin Kirista na gaskiya da zai yi ta’addanci ko tare matafiya ya sheke su kuma ya iya kafa hujja a BIBLE. Kazalika kawo kabila ko ƙabilanci a lamuran ta’addanci mugun zalunci ne da wasu ke yi don cimma muradin ƙiyayya da ta yi kanta a zuciyarsu. Kama daga maciyin amana Chukwuma Nzeogwu da ya buɗe wuta a gidan firimiya Sir Ahmadu Bello ya bindige Sajan Daramola Oyegoke don kin amincewa ya harba babbar bindigar tankar yaƙi don ruguje gidan Arewa da Sardauna ke ciki kowa ma ya mutu; ya shiga gidan ya bindige Sardauna har hakan ya shafi matarsa Hafsa. Duk wanda zai aikata haka ba tare da la’akari da sakamako mai muni da zai biyo baya ba bai kamata a sanya shi a jerin masu hankali ba. Cin amana muguwar ɗabi’a ce da kan yi ta bin wanda ya yi ta har ƙarshen rayuwarsa. Jinin manyan jagorori irin Gamji ba kaɗai haƙƙin danginsa ba ne, a a ya shafi dukkan al’ummar Arewa da masu son rayuwar ‘yanci bayan tafiyar ‘yan mulkin mallaka. Tun zubar da jinin iyayen kasa a 1966 a ke ta neman bakin zaren dawo da ƙasa kan turba don yadda a ka haddasa ƙiyayya tsakanin al’umma da kirarinta “ƙasa ɗaya al’umma ɗaya”
Mu gangaro kan Nnamdi Kanu wanda ya yi ta hura wuta lallai sai mutanensa sun ɗau makami sun yi ta kashe-kashe don a kafa Biyafara da ƙarfin tsiya. Ya yi sanadiyyar kashe ɗaruruwan mutane ciki da jami’an tsaro da ‘yan Arewa musamman Hausawa. Sai kwatsam yayin yanke ma sa hukunci, ’yan iƙirarin Hausa zalla su ka yi tsayin daka har da kiran zanga-zanga wai lallai sai an sake shi. Ba mu yi mamaki ba don dama Kanu ya kwan biyu ya na kiran a hargitse da yaƙi a Arewa. Kanu ya dawo da batun kafa Biyafara bayan madugunta Ojukwu ya yi gargaɗin cewa hakan ba shi da muhimmanci. Har dai wani na ganin ya na son yankinsa ya balle, ai sai ya bi tsarin dimokuraɗiyya da doka ta hanyar neman a yi zaɓen raba-gardama.
Duk ɓarayin dajin nan na da manyan magabatansu da su ka koyo dabarun satar mutane daga wajensu da samun miyagun kwayoyi da makamai. Kun tuna ƙasurgumin mai satar mutane da safarar miyagun ƙwayoyi Chukwudumeme Onwuamadike wanda a ka fi sani da EVANS ya fi kowa shahara da satar mutane kuma an cafke shi a 2017 bayan a ɗaya daga ayyukansa ya nemi fansar dala miliyan 2. Hamshaƙin mai hannu da shuni ne na kuɗin jini kuma haifaffen Nnewi da ke jihar Anambra. DSP Abba Kyari ya cafke shi kuma an gurfanar da shi gaban kotu a Lagos da samunsa da laifi. Ya yi sanadiyyar kashe mutane da daman gaske.
Cikin miyagun masu kashe mutane ba gaira ba dalili akwai kwamandan IPOB Ifeanyi Eze Okorienta wanda a ka fi sani da GENTLE DE YAHOO wanda ke jagorantar kashe-kashe a gungun rundunar kisan gilla ta IPOB wato ESN. In ransa ya ɓaci ya kan bindige hatta yaransa kamar yadda mu ke gani a fim din Indiya. Mu dawo nan Binuwai mu tuno ta’addancin satar mutane da kisan gilla barkatai na Tarwase Akwaza da a ka fi sani da Gana haifaffen Gbeji da ke Katsina-Ala a jihar Binuwai. Gana don tsananin kashe-kashe har a na cewa ya kan ɓace ɓat ya bayyana kuma in an ambaci sunansa mutane kan shiga rawar ɗari da firgita don dan-gayawa-jini-na wuce ne. Da kyar sojoji su ka yi nasara a kan sa a 2020.
A Arewa maso yamma da Arewa ta tsakiya an fara samun matsala ne bayan lafawar Boko Haram a Arewa maso gabar. Mun san miyagu da su ka bunƙasa daga satar shanu zuwa satar mutane. Hakika a Arewa da can sai dai ‘yan kwanta-kwanta a kan titi ba ma wasu gaggan ‘yan fashi ba duk wannan an yi simogan ɗabi’ar daga kudu ne. Al’ummar musamman jihar Zamfara za su fi zama shaida kan yadda matsalar nan ta fara har ta zama gagarumar matsalar tsaro.
Mun san labarin Buharin daji wanda tuni ya sheka lahira. Ga Dogo Gide, ga Halliru Sabubu na lahira, ga Kachalla Ali na lahira, ga Baleri na lahira da sauran su da lokaci ne kawai a ke jira. Sunan wanda ya fi shahara a kafafen labaru Bello Turji wanda ƙaramin yaro ne da har banan na shekarunsa 32 don an haife shi a Shinkafi jihar Zamfara a 1994. Har fa a ka gama yaƙin Saddam na farko ba a haife shi ba. Har a ka yi yunƙurin juyin mulkin Gideon Orkar ba a haife shi ba, har a ka yi zaɓen 12 ga Yuni 1993 na Abiola ba a haife shi ba. Mu na fatan ranar da ya gamu da gamonsa a samu zaman lafiya mai dorewa. Wato abun da ke damuna yaranmu da wasu ma Turji ya grime su nesa ba kusa ba don akwai wanda bana ya ke 18-20 amma su ke hawa soshiyal midiya su na zunduma ashar don ba su san tarihin Arewa ba sai karyar da su Nnamdi Kanu su ka shayar da su ta yanar gizo da ƙiyayya ta ba gaira ba dalilin adalci da su ka samu daga iyayensu da jama’ar ƙauyukansu.
Ba yadda za a yi Bahaushe ya zama Nnamdi Kanu ne zai faɗawa ma sa abun da zai yi ko wasu Gwarawa da su ka ɗinka rigar karya ta Hausawa ne wai za su haska mu su yadda za su yi rayuwa. Kullum su kan jefi duk wanda su ke son a hallaka da kalmar AGWAI wacce ba Hausawa ke amfani da ita wajen ambaton Fulani ba, kalma ce ta kabilun Arewa ta tsakiyar Nijeriya da miyagu ke kira MIDDLE BELT. Wallahi ba fada tsakanin Hausawa da Fulani amma akwai ƙiyayya ga Hausawa daga maƙiya Musulunci da ke jin haushin ƙarfin riko da addinin Musulunci na Hausawa.
Shin su waye su ka kashe Musulmi Hausawa a Zangon Kataf, Gonin Gora, Zaki Biam, Yelwan Shendam, Riyom da sauran sassa? Amsa ‘yan basajar nan ne dai maƙiya al’ummar Arewa da ke matuƙar ƙaunar iyayensu da ba su shuka alheri.
Bayan Turawan mulkin mallaka sun shigo sun karkashe dukkan wadanda su ka ki mika mu su wuya don shan taba da rawar banjo, su ka kafa tsarinsu na duniya hayakin taba da feke gashin baki kamar Mr.Muzuru da aske gemu tatas kamar Mr.Shafumulera, sun mika mulki ga ‘yan ƙasa masu kishi na larduna 3 a 1960. Wannan bayan haɗe Arewaci da Kudanci a matsayin Nijeriya a 1914 da Gomna Frederick Lord Luggard wato Gomna Lugga a takaice ya jagoranta. Me ya sa ‘yan IPOB na farko su Nzeogwu da Donatus Okafor su ka kashe manyan jagorori na Arewa da su ka haɗa da Sir Ahmadu Bello da Firaminista Abubakar Tafawa Balewa? Idan dalilin masu kare kisan gilla ga Gamji cewa ya nuna Igbo ‘yan mamaya ne, shi kuma Sir Tafawa Balewa me ya ce?
‘Yan IPOB na farko fa ƙarƙashin Donatus Okafor sun fara da kai farmaki gidan Burgediya Zakariya Maimalari a Thompson Avenue a Ikoyi. Da farko Maimalari ya ankara ya kauce amma kash ya fada hannun wani dan IPOB din Emmanuel Ifeajuna da tsammanin ba maciyin amana ba ne. Ifeajuna da wani mugun Ezedigbo su ka bindige Maimalari. Ifeajuna ne ya sace Firaminista ya fice bayan garin Lagos su ka yi ma sa kisan gilla kuma sai ma bayan kwanaki a ka gano gawarsa har ta fara canjawa!.
Mugayen mutane da su ka hana Nijeriya zaman lafiya su ne ‘yan Biyafara/IPOB da su ka maida zubar da jinin waɗanda ba su yi mu su laifin komai ba a matsayin aikin gwagwarmayar kare muradun al’ummar Igbo. Duk neman shashantar da wannan tarihin na zubar da jini ya sa IPOB amfani da ‘yan ƙaryar Hausa zalla don yayata farafaganda a Arewa ta nuna Hausawa daban Fulani daban. Mun ma godewa Allah da Farfesa Aliyu Muhammad Bunza ya ce sam yanzu ba wanda ya isa ya bugi ƙirji ya ce shi Bahaushe ne 100%.
KAMMALAWA
’Yan ƙaryar Hausa zalla da su ka fito daga ƙananan ƙabilu masu tare hanya su kashe matafiya su kona da ma wasu Maguzawa da yarensu ya ɓace ɓat a tarihi su ka narke zuwa Hausawa, ke ɗinka rigar Hausawa don cimma burin wannan kwangila su na cika tumbinsu da kuɗin jinin haram kuma tabbas za su yi aman jinin.
Haka kawai wani dan sullutun yaro sai ya fito a shafin soshiyal midiya da sunan karya ba hoto wai ya na kare muradun Hausawa. Yaran da manyan na jami’a za su sha mamaki kuma za su yabawa aya zaƙi. Ba za mu taba mantawa da kisan gillar da a ka yi wa Gamji da Firaminista ba. Da yardar Allah za mu gadarwa na baya ma wannan tarihi don su san yadda za su zauna da ‘yan Biyafara.
