
Shugaban Ƙaramar Hukumar Bichi, Alhaji Hamza Sule Maifata ya ƙaddamar da ayyukan raya ƙasa a wurare daban-daban na yankin ƙaramar hukumar.
Ayyukan raya ƙasar, sun ƙunshi gyara da gina magudanan ruwa a unguwani da suka haɗa da; unguwar Zango da Maƙera da kuma Dakali.
Haka ɓangaren gadoji, Shugaban yankin, Alhaji Hamza Maifata, ya sabunta gadar gaban Ofishin Hisba da Hukumar Ilimin Firamare na yankin (LEA) tare da gadar bakin masallacin ‘yan Izala dake kan titin Gwarzo, dukkansu a ƙaramar hukumar.
Kazalika, Alhaji Hamza Sule Maifata, ya samar da wasu sababbin gadoji guda uku; a kan titin gidan Ibrahim Mu’azzamu da kuma tsakanin Kanti Firamare tare da Gundala.
A hannu guda na labarin Shugaban Majalisar yankin, Alhaji Hamza Maifata ya kai ziyarar gani da ido ga wasu sababbin ayyukan magudanan ruwa da Ɗanmajalisar Tarayya mai Wakiltar Bichi, Alhaji Abubakar Kabir Abubakar yake gudanarwa a unguwar Kanti, tare da kuma sabuwar gada da yake aiwatarwa a ƙofar gidan Sufeto Bala mai ritaya a Bichi.
