Kano: Gwamna Abba ya ɗauki surukin Atiku, Murtala Garo a matsayin mataimaki

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya zaɓi Alhaji Murtala Sule Garo a matsayin sabon mataimakin gwamna bayan saukar Kwamared Abdulsalam Gwarzo a muƙamin.

Rahotanni sun bayyana cewa, Abdulsalam Gwarzo ya yi murabus ne bayan ɓarkewar rikici tsakaninsa da gwamnan a lokacin da ya (Abba) fice daga jam’iyyar NNPP ya koma APC mai mulki.

Wannan al’amari ya haifar da tsama a dangantakar aiki ta mutanen biyu, inda tsohon mataimakin gwamnan ya shiga halin matsi na ya bi gwamnan amma kuma ya tirje akan ƙin amince wa hakan.

Akan ƙamarin rikicin nasu ne majalisar dokokin jihar ta fara yunƙurin tsige Gwarzo. Ana tsaka da haka ne ya ɗauki matakin yin murabus, sannan kuma ya fice daga NNPP ya koma ADC.

Da yake sanar da ci-gaban, Babban Sakataren yaɗa labaran gwamnan, Mustapha Muhammad, ya tabbatar da cewa an fitar da sunan Garo a matsayin wanda zai zama sabon maitaimakin.

Murtala Garo wanda sanannen ɗan siyasa ne a Kano, yana auran Walida Atiku Abubakar, wato ɗaya daga cikin ‘ya’yan tsohon mataimakin shugaban ƙasa kuma jigo a jam’iyyar adawa ta ADC, Atiku Abubakar.

Gwamnatin jihar ta bayyana ɗan shekara 48 ɗin a matsayin ƙwararren ɗan siyasa mai ƙwarewar sama da shekaru 20 a muƙaman zaɓe da naɗi a jihar, tana mai cewa ta yi haka don inganta lamuran gudanar da harkokin hidimta wa al’ummar jihar.

By Babaji