Hukumar tace fina-finai a Kano ta rufe shagon maganin gargajiya kan tallan batsa

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano ta ɗauki matakin gaggawa kan wani mai sayar da maganin gargajiya da ake zargi da amfani da wasu ƙananan yara a cikin wani talla mai ɗauke da kalaman da ba su dace ba.

Hukumar ta bayar da umarnin rufe shagon mai sayar da maganin gargajiya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da ta samu.

Kazalika, shugaban hukumar, Alh Abba El-Mustapha, ya gayyaci mai saida maganin wanda ake kira da Nagwale domin ya bayyana a gaban hukumar domin amsa zarge-zargen da ake yi masa.

Da yake jawabi kan lamarin, daraktan da ke lura da sashin ɗab’i na hukumar Alh. Zakari Garun Babba ya bayyana cewa sayarwa da kuma tallata irin waɗannan magunguna a bainar jama’a, musamman idan sun haɗa da yara ko abubuwan rashin kunya, laifi ne kuma yin hakan ka iya jawo tsauraran hukunci a ƙarƙashin doka.

Ya ƙara da cewa wanda ake zargin ya amsa laifinsa tare da neman afuwa ga al’ummar Jihar Kano. A matsayin wani ɓangare na matakan ladabtarwa na hukumar, an umurci Nagwale da ya bayar da uzuri a rubuce, da sauti, da kuma bidiyo, domin a adana su a matsayin wata hujja a nan gaba.

Hukumar ta jaddada cewa doka ce ta bata dama domin sa ido kan ayyukan masu sana’ar maganin gargajiya, musamman a fannin talla, domin tabbatar da bin ƙa’idojin ɗab’i.

Hukumar ta Jihar Kano ta sake jaddada aniyarta na kare tarbiyyar al’umma da kuma kiyaye yara daga duk wani nau’in cin zarafi.

By ukarofi