Tare da BILKISU YUSUF ALI, PhD
Mata da yawa idonsu ya kan rufe kan cewa, duk namijin da ya zo wurinsu da sun fara soyayya sai su zata wanda ya zo wurin nasu aure ne ya kawo shi. Amma da tafiya ta yi tafiya sai su nemi saurayin su rasa. Wannan yana cikin babbar hujjar da ta sanya da yawan mata na kallon maza mayaudara, saboda ƙin auren su duk kuwa da soyayyar da suka sha, amma a ƙarshe sai ka ji sun ce “wai suna neman mace ta gari ne uwar ‘ya’yansu, ba matar aure ido rufe ba.” Amma duka kowanne ɓangare sun yarda da karin maganar nan ta Bahaushe ta ƙwarya ta gari na ragaya. Maza sukan zama a ruɗe yayin da suka tashi neman mace ta gari har sukan shiga shakka kan wace ce macen da ya dace su aura. Amsar da suke samu ita ce, su yi duk inda za su yi su lalubi mai kamun kai, daga ita ne ake samun mace ta gari. Ita kuwa mai kamun kai siffofinta a bayyane suke, wacce idan namiji ya ƙura ido ya tsananta nema, to za a dace.
Mace ta gari ita ce macen da Bahaushe ke kira mai kamun kai wacce ta siffantu da kyakkyawar ɗabi’a da halaye da kamala, kallo ɗaya za a iya gane tarbiyyarta da ƙoƙarin da iyayenta suka yi wajen ba ta tarbiyya. Mace ta ƙwarai ita ce wadda kowanne namiji mai hankali zai yi fatan a ce tana gidansa ta zame masa sanyin idaniya ta zama al-mar’atissaliha da Annabi Muhammad (SAW) ya ce, ta fi duniya da duk abin da yake cikinta. Mace ingantacciya ita ce dai matar da kowanne namiji zai so ya sami zuriya da ita.
Mata da dama da za ka tattauna da su shine babbar matsalarsu mijin aure, abin haushi da ke damun su ga masoyan nan kamar jamfa a Jos, amma auren ya gagara. Mata na ta wahalar addu’a da ’yan dabaru duk ana ta fama, amma abu ya ƙi yi wuwa. Tashin hankalin ba ga ’yan matan ba, ba kuma ga zawarawan ba. Mace wadda ba ta da makusa ta kowanne ɓangare; kyau ko asali ko ilimi, amma aure ya gagara ana ta laluben dalili an kasa gano gaskiya abu guda ke zagayawa a ƙwaƙwalwarsu shine maza mayaudara ne, amma fa duk yaudararsu suna neman mace ta gari ne, don sawa a ɗaki. Abubuwa da maza kan duba yayin zaɓen mace suna da yawa, amma dai mafi muhimmanci sune:
Kamun kai
Idan ka tashi neman matar da za ka aura ka dage ka nemi mai kamun kai. Yana cikin matakin farko da namiji ya kamata ya fara lura yayin ƙulla aure. Hanyoyi da dama za ka lura da shi in kana son gane mace mai kamun kai kada ka jira a ba ka labari kai da kanka za ka sa ido ka lura. Mata a yau a tunaninsu yadda suke ganin maza na haba-haba da mata ba tare da nuna wani zaɓe ba to su sani iyakar ta waje ne. Don haka kai mai neman aure ka sa lura na zaɓen mace mai kamun kai. Abubuwa da dama da za ka tabbatar da wannan tana da kamun kai akwai:
Sutura
Sutura ita ce abin da ake sanya a jiki don kare tsiraici. A sutura ana gane kamalar mutum. Abu na farko da kan ja hankalin namiji ga mace har ya gane ajin da zai ajiye ta shi ne irin suturar da ta saka jikinta. Mata a yau suna tunanin bayyana tsiraicinsu shi ne hanyar da za su iya janyo hankalin namiji gare su har ya gane kyan wani bangare na jikinsu da zai kai su ga aure. Kai da ka ke neman abokiyar rayuwa ka nutsu ka nemi wadda ka yaba da shigarta ta kamala ba ballagaza ba, Yana da kyau mace ta yarda da cewa mijinta duk inda yake zai tarar da ita sannan ba wani dace da za a samu a saɓon Allah. Don mata da yawa suna bayyana tsiraici ne don jan hankalin namiji.
Surutu
Surutu barkatai alamu ne na rashin kamun kai macen kwarai ba a santa da ɗaga harshe ba, ko da a cikin ‘yan’uwanta mata ne bare kuma maza. Wata matar tana tunanin in ta shiga dandazon maza ta daga muryarta da zaƙewa shi ne zai janyo hankalin namiji kan su. Mace mai surutu rau-rau a kan titi ko cikin maza ba ta cikin irin matar da ka ke nema ka aura. Mace mai kamewa da ƙarancin Magana ko da kuwa a wajen saurayin ne abar yabo ce da soyuwa ko da batun auren ne irin su ake nema a adana a gida
Kunya
Bahaushe ya ce “kunya marin ɗa”. Ka tabbatar matar da za ka aura mai kunya ce don kuwa duk macen ta gari an santa da kunya da yakana da kara. Mace ba ta isa mace abin sha’awa in har ta zamanto fitsararriya.
Akwai hanyoyi da dama da mace za ta nuna kunya. Daga ciki akwai ciye-ciye. Mata a yau sun zubar da kyakkawar al’adar nan ta kame kai wajen ciye-ciye a kan hanya ko gaban samari. Mace mai ciye-ciye da rashin kimtsi ko ga sa’anninta mata ba ta farin jini bare maza. Duk matar da ka ganta tana ciye ciye kan turba bar ta kawai ba ta shirya samun mijin aure ba.
Bayan ciye-ciye akwai roƙo. Roƙo shi ma wata hanya ce ta nuna rashin kunya da mata kan ɗauka hanya wayewa. Duk matar da ta fiye roƙo tana kashe wa kanta wata daraja ne ga mai sonta kuma in har mace ta fiye roƙo to fa tana nunawa wannan da zai aure ta irin zaman da za su yi. Hali na farko da za su sa a ran su in har suka kai ki gidansu ba za ki iya haƙuri da samu da rashi ba, sannan duk randa babu ba za ki iya rufa wa zamantakewar asiri ba. Roƙo ga mace babbar hanya ce ta zubar da mutunci. Don haka in budurwarka ta ishe ka da ba-ni-ba-ni na ba gaira ba dalili to fita a guje ba ba matar aure ce ba.
Abu na gaba shi ne kallo. Don a kallo kaɗai ana iya bayyana halin mace da tarbiyyarta da kunyarta da dacewa ta a kai ta gida ko kuma ba za ka kai ta ba. Ka lura da yadda wadda za ka aura take kafe ka da ido ba rusanawa, lallai to ka bi a sannu.
Rashin jan aji ga mace shi ma babbar illa ce da za a iya kyale ta a macen da ta dace a aura. Mace ta kirki da jan aji da kamewa aka santa. Ba wai ta zama mai girman kai ba amma ka nemi wanda ta san darajar kanta. In har mace za ta zama arha kowanne namiji ya kira ta ba tantancewa ta je, kowa yake buƙatar jin hira ko yawo ita za a zo nema a tafi da an ce ana sonta to fa kasuwa ta bude ba sauran eɗcuse to fa mai irin wannan halin za ta jima wurin neman mijin aure. Kai ma mai neman matar ƙwarai kada ka leƙa.
Zafin soyayya ma yana da nashi illar idan har an faɗa babu lura. A nan ba sai na yi dogon sharhi ba, ku maza ku ne ku ke lallaɓawa ku nemi yarinya da buƙata ta biya ba kwa kuma komawa. Mu a ɓangarenmu mata sai mu ce rashin alƙawari ne ya janyo haka, amma ku kuka san dalili, don haka ni a nan ba ni da ta cewa. A wannan gaɓar ya rage wa matan tunda sai me ƙarfin rabo ce saurayi ke neman ta a ƙarshe ya aure ta. Na san zai yi wuya ko na ba ka shawarar idan haka ta afku duk da ba a fata ko na ce ka aure ta ba na ji za ka iya.
Abin nufi dai da wannan rubutu shi ne ƙwarya ta gari na ragaya. Maza irin wannan suke nema su kai gida. ƙalubale ne ga iyaye su sa ido kan tarbiyyar ‘ya’yansu sannan su ke nusar da su abubuwan da ya dace na tarbiyya. Allah ya sa mu dace amin.
Mu haɗu a mako na gaba da yardar Allah
