Kano: Mutane fiye da 200 ne suka samu tallafin jari a Mariri

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

Mutane sama da dari biyu maza da mata ne suka amfana da tallafin kuɗi na N20,000 kowannensu domin gudanar da sana’o’in dogaro da kai, daga Kansilan Mazabar Mariri, kuma Shugaban Majalisar Kansilolin Kumbotso, Hon. Nafi’u Alhassan Garba Roja.

Hon. Roja ya bayyana cewa wannan tallafi yana cikin ƙudirin Gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf, wanda ke da nufin tallafawa jama’a musamman matasa da talakawa domin rage zaman banza da dogaro da wasu. Ya ce, “Mun ɗauki wannan mataki ne domin karfafa sana’o’i da tabbatar da cewa mutanenmu suna da abin dogaro da kansu.”

Ya roƙi waɗanda suka amfana da su yi amfani da tallafin ta hanya mai kyau, domin su ma wata rana su taimaka wa wasu. “Duk wanda bai ji sunansa ba, to ya yi hakuri, akwai wani shiri na gaba, kuma gwamnati tana sane da bukatun jama’a,” inji shi.

Hon. Roja ya gode wa Gwamnan Jihar Kano bisa yadda yake ba su damar gudanar da ayyuka kai tsaye a mazaɓu, tare da miƙa godiya ga Shugaban ƙaramar Hukumar Kumbotso, Hon. Ghali Abdullahi Shitu Basaf, bisa goyon bayan da yake baiwa kansiloli wajen ciyar da ayyukan raya ƙasa gaba.

A nasa jawabin, Mai ba Gwamnan shawara kan siyasa, Hon. Sunusi Surajo Kwankwaso, ya jinjinawa Hon. Roja bisa wannan ƙoƙari, yana mai cewa ya zama abin koyi ga sauran shugabanni. Ya kuma buƙaci masu riƙe da muƙaman siyasa su riƙa gudanar da irin wannan ayyukan domin ciyar da matasa gaba.

Shi ma Shugaban ƙungiyar Shugabannin Kansiloli (Speakers Forum) kuma Shugaban Kansilolin Wudil, Hon. Bashir Shehu Aliyu Acika, ya yaba da wannan shiri, yana mai gargadin waɗanda suka samu tallafin da kada su yi sakaci da abin da aka basu.

Taron rabon tallafin ya samu halartar shugabannin siyasa daga ƙananan hukumomi daban-daban, kansiloli, da al’umma, kuma ya gudana a Dutse Royal Hall, titin Maiguru, Kano.

By ukarofi