Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Masana harkar kiwon lafiya sun ɗora alhakin cunkoson marasa lafiya a manyan asibitocin gwamnati ga rashin ingancin cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko (PHC) a ƙasar nan, suna masu cewa matsalar na janyo ƙarancin gadon kwanciya da tsaikon kula da marasa lafiya a matakai biyu da uku na jihohi da tarayya.
A tattaunawa da manema labarai a Legas a ranar Litinin, ƙwararrun sun ce ana ci gaba da ganin ɗaruruwan mutane na kwararowa zuwa manyan asibitoci domin neman kulawa, duk kuwa da cewa yawancin lamurran lafiyar da suke kai su can za a iya magance su a matakin PHC.
Dakta Livinus Abonyi, Dekan Fannin Kiwon Lafiya a Jami’ar Allied Health Sciences ta Tarayya da ke Enugu, ya ce lokaci ya yi da Nijeriya za ta ƙarfafa cibiyoyin lafiyar farko ta hanyar ƙara musu kayan aiki, ƙwararrun ma’aikata da kuma ingantaccen ayyuka.
Ya nuna damuwa kan yadda yawancin PHC ke fama da ƙarancin ma’aikata, ƙarancin kayan aiki da rashin isasshen tallafin kuɗi, lamarin da ya ce ya tauye aikinsu wajen kula da al’umma yadda ya kamata.
Ya ƙara da cewa, wajibi ne PHC su kasance suna aiki awanni 24 a rana, domin galibin gaggawar lafiya kan faru ne da dare, kuma rashin waɗannan ayyuka a matakin farko na tursasa jama’a zuwa manyan asibitoci.
Abonyi, wanda shi ma Farfesa Mai Rasuwa ne a fannin Medical Radiography/Medical Imaging, ya jaddada cewa cunkoson jama’a a manyan asibitoci ya kai ga rashin isassun gadon kwanciya, inda marasa lafiya ke yawan zaune a ɗakunan jiran likitoci ko kuma a kan kujera saboda babu gurbi.
A cewarsa, idan cibiyoyin lafiya na farko za su yi aiki yadda ya kamata, ana iya magance kaso mafi yawa na matsalolin lafiya a can, sannan kashi kimanin 30 cikin 100 kacal za su shiga manyan asibitoci domin samun kulawa musamman ta kwararru.
Ya yi kira ga gwamnati da ƙungiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu da su hada hannu wajen inganta PHC, ganin cewa su ne ginshiƙin tsarin lafiya kuma tudu na farko da jama’a ke dogaro da shi.
