Ban taɓa ganin uwargida mai sa’a kamar uwargidan Gwamna Raɗɗa ba – Sarkin Daura

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, ya bayyana cewa bai taɓa ganin uwar gida mai sa’a da natsuwa irin Uwargidan Gwamnan Jihar Katsina, Hajiya Zulaihat Dikko Umar Radda ba.

Ya ce Hajiya Zulaihat ta samu baiwar Allah ta musamman da ke bayyana a cikin jajircewarta wajen gudanar da ayyukan taimako ga al’umma, musamman mata da marasa galihu.

Sarkin ya bayyana hakan ne a fadarsa da ke Daura, yayin da yake karɓar gaisuwar godiya daga Uwargidan Gwamna Radda, wadda ta kai masa ziyara domin nuna godiya bisa nadin sarautar “Jagabar Matan Kasar Hausa” da aka ba ta a kwanakin baya.

A cikin jawabinsa, Sarkin Daura ya yabawa Uwargidan Gwamnan bisa kyawawan dabi’u, sanin ya kamata, da jajircewa wajen tallafawa al’umma. Ya kuma jaddada cewa irin wannan hali ne ya kamata sauran mata su yi koyi da shi domin samun zaman lafiya da ci gaba a cikin al’umma.

“Wannan ziyarar da kika kawo alama ce ta ladabi da godiya. Na yaba da irin tarbiyyar ki da yadda kike gudanar da aikinki cikin natsuwa da biyayya. Ki ci gaba da wannan tafiya mai albarka, domin abin koyi ce ga sauran mata,” in ji Sarkin Daura.

Sarkin ya kuma ba ta izinin nada wasu sarautu ga mata a matsayinta na “Jagabar Matan Kasar Hausa,” ya ce.

“Na baki dama idan kin koma gida, ki iya nada duk wata sarauta da kika ga ta dace. Ki fara da matar Mataimakin Gwamna, Hajiya Asma’u Faruk Lawal Jobe.”

A nata jawabin, Hajiya Asma’u Faruk Lawal Jobe ta bayyana farin cikinta da wannan nadin, tana mai cewa Uwargidan Gwamna ta cancanci wannan karramawa saboda jajircewarta wajen inganta rayuwar mata a jihar Katsina.

“Uwargidan Gwamna Hajiya Zulaihat ta cancanci wannan sarauta saboda halayenta na kirki da himmarta wajen tallafawa mata da marasa ƙarfi.

Taron ya gudana cikin nishadi da girmamawa, inda manyan mata ‘yan majalisa, shugabannin ƙananan hukumomi, jami’an gwamnati da abokan arziki suka halarta.

Wadanda suka halarta sun taya Uwargidan Gwamna murna tare da yi mata fatan Allah Ya ƙara ɗaukaka tafiyarta da albarkace ayyukanta na alheri.

By ukarofi