
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Juma’a ne Kantoman Ribas, Ibok-Ete Ibas ya bayyana a gaba kwamitin Majalisar Wakilai da ke kula da dokar ta-ɓaci a jihar.
Ana gudanar da zama da shi ne a yanayi na sirri, wanda kwamitin mai mutane 21 ke jagoranta.
Kakakin Majalisar, Tajuddeen Abbas ya naɗa kwamitin a ranar 15 ga watan Afrilu, ya na mai tabbatar da cewa za su yi adalci wajen tabbatar da bin tsarin dokar ƙasa a halin dokar ta-ɓaci a jihar.
Ibas ya gabatar wa kwamitin ba’asi ne game da jagorancinsa a jihar, inda ya bayyana cewa ya na ƙoƙarin sauke nauyin da aka ɗora masa bisa gaskiya da adalci.
Ya kuma nemi kwamitin da ya ƙara ba shi haɗin kai don ganin ya sauke nauyin shugabancin nasa bisa daidai.
Majalisar ta na shirin aiki ne da hukuncin doka da ya ba ta damar karɓe iko da majalisar dokokin jihar.
A ranar 18 ga watan Maris ne Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Ibas a matsayin kantoman Ribas biyo bayan dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Udo da ƴan majalisar dokokin jihar da ya yi.
