
Daga BELLO A. BABAJI
Kantoman Jihar Ribas, Ibok-Ete Ibas ya halarci taron Majalisar Tattalin Arziƙi ta Ƙasa, NEC, a Fadar Shugaban Ƙasa dake Abuja, ƙarƙashin jagorancin Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima.
Baya ga shi, akwai gwamnoni da wasu mambobin majalisar da suka halarta, wanda karo na farko kenan da ya samu zuwa tun bayan naɗa shi kantoman da Shugaba Bola Tinubu ya yi a watan Maris.
Shugaba Tinubu ya naɗa shi ne sakamakon ƙamari da rikicin siyasar jihar ya yi, lamarin da ya sa aka dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Farfesa Ngozi Udo da ɗaukacin ƴan majalisar dokokin jihar na watanni shida.
Hakan ya haifar da cecekuce da tattaunawa game da halascin hukuncin shugaban ƙasar a dokance.
A karo na biyu, mata sun sake fitowa titunan Farakwal a ranar Alhamis, inda suke gudanar da zanga-zangar neman a dawo da dakataccen Gwamna Fubara da sauran zaɓaɓɓun jami’an gwamnatin jihar da aka dakatar kan muƙamansu.
