Kamfanin sadarwa na MTN, wanda shi ne mafi girma a nahiyar Afirka, ya tabbatar da cewa ya fuskanci kutse daga ‘yan kutse na yanar gizo da suka samu damar shiga rumbun adana bayanai na kanfanin. Duk da haka, kamfanin ya bayyana cewa muhimman bayanai kamar tsarin biyan kuɗi da hanyoyin sadarwa ba su samu wata barazana ba.
A cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafinsu, MTN ta ce tana gudanar da bincike domin gano irin tasirin da kutsen ya yi, kuma ta bayyana cewa ba a samu wata alama da ke nuna cewa an saci bayanan kuɗi na abokan ciniki ko asusun dijital ba. Haka kuma, sun sanar da hukumomin tsaro ciki har da rundunar ‘yan sanda ta Afirka ta Kudu da rundunar Hawks domin taimakawa da bincike.
Kamfanin ya ce yana cikin shirin sanar da abokan cinikin da lamarin ya shafa, kamar yadda dokoki da ƙa’idojin ƙasa suka tanada. Har ila yau, MTN ta shawarci abokan ciniki da su kare kansu ta hanyar sabunta kalmomin sirri, guje wa latsa hanyoyin da ba su da tushe a saƙonni, da kuma amfani da kariya ta mataki biyu (two-factor authentication).
MTN, wanda ke da sama da abokan ciniki miliyan 280 a ƙasashe 19, ya buƙaci mutane da kada su bayyana sirrukan shiga kamar PIN, kalmar sirri ko OTP ga kowa ta hanyar waya, saƙon rubutu ko imel. Kamfanin ya bayyana ƙudurinsa na ci gaba da aiki da hukumomin tsaro da na gwamnati domin daƙile tasirin wannan hari.
