
Daga BELLO A. BABAJI
Majalisar Tattalin Arziƙi ta Ƙasa, NEC, ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ta sake dakatar da tattauna batun kafa ƴan sandan jihohi.
A zamanta na ranar Alhamis, majalisar ta ce ta yi hakan ne sakamakon rashin wadataccen lokaci na tattauna batun, kamar yadda Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Fito ya bayyana wa manema labarai.
Ya kuma tabbatar da cewa, za a bai tattauna batun muhimmanci sosai a yayin zama na gaba.
Zaman ya ƙunshi Shettima a matsayinsa na Shugaba, sai gwamnoni ciki har da kantoman Ribas, wato Ibok-Ete Ibas.
Haka kuma Ministan Abuja, Nyesom Wike da Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Yemi Cardoso sun halarci zaman.
Tun a ƙarshen shekarar 2023 ne aka jinkirta tattauna batun kasancewar jihohi ba su kammala bada rahoton matsayar su ba game da kafa ƴan sandan, wanda an faro ne da nufin daƙile ayyukan ta’addanci da suka yawaita a sassan ƙasar.
A watan Nuwamban 2024 ne baki daya ɗaya jihohi 36 har da Abuja suka kammala miƙa rahotannin matsayarsu kan batun ga majalisar.
