Karfa-ƙarfa aka mana wajen amincewa da sassan dokar zaɓe – Tambuwal

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya zargi shugabancin Majalisar Dattawan Najeriya da yin ƙarfa-ƙarfa wajen amincewa da wani sashe na dokar zaɓe ba tare da yin gyara ba, yana mai cewa an yi hakan ne duk da adawar ɓangaren marasa rinjaye.

A hirarsa da BBC, Tambuwal ya ce hatsaniya ta ɓarke ne a zauren majalisa sakamakon yadda aka ƙi amincewa da buƙatar ‘yan adawa na a sake duba sashen dokar.

A cewarsa, abin da aka fara gabatarwa shi ne buƙatar hukumar zaɓe ta sauya kwanakin bayar da sanarwa daga kwana 360 zuwa 300 domin daidaita jadawalin da ya faɗo a lokacin azumin shekara mai zuwa.

Ya ƙara da cewa, “Karfa-karfa aka mana wajen amincewa da wani sashe na dokar zaɓe,” yana mai cewa bayanan da suka samu sun nuna shugabannin majalisun biyu da kwamitocin daidaito sun zauna tare da cimma matsaya inda aka fi karkata ga abin da majalisar dattawa ta amince da shi.

Tambuwal ya ce “a lokacin ne muka nuna rashin amincewa” inda ya ce dole ne a bari a yi zaɓe a fili domin kowa ya bayyana matsayinsa.”

Ya kuma jaddada cewa ” Kuma muna ganin hakan hakan zai ba da wata hanya ta yadda za a iya yin magudin zabe wanda shi ake kokarin a kaucewa

Ce-ce-ku-ce kan dokar zaɓe a Najeriya na ci gaba da ɗaukar hankali, musamman bayan hatsaniyar da ta taso a zaman haɗin gwiwar majalisun biyu kan batun bayyana sakamakon zaɓe ta rubutu a wuraren da babu intanet, lamarin da ya ƙara rarraba kawuna tsakanin ɓangarorin siyasa.

By ukarofi