Zaɓen Abuja: INEC ta sanar da wanda ya lashe zaɓen Gwagwalada

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta sanar da Mohammed Kasim na Jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen Ƙaramar Hukumar Gwagwalada da ke Abuja, wanda aka gudanar a jiya Asabar.

Farfesa Philip Akpeni, wanda shi ne Baturen zaɓen ƙaramar hukumar, ya sanar da haka a safiyar yau Lahadi.

Da yake sanar da sakamakon, Farfesan ya bayyana cewa, Kasim ya samu ƙuri’a 22,165 don haka aka ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen.

Ya kuma ce, wanda ya zo na biyu shi ne ɗan takarar Jam’iyya mai mulki (APC), wato Yahaya Usman, wanda ya samu jimillar ƙuri’u 17,788, yayin da Biko Umar na APGA ya samu ƙuri’a 1,687 a matsayi na uku.

An gudanar da zaɓen ne a gundumoni goma da suka haɗa da Paiko, Dobi, Gwako, Ibwa, Staff Quaters, Zuba, Ikwa, Kutunku, Gwagwalada Centre da kuma Tunga Maje.

By Babaji