Kashe-kashen Benuwai: Hukumomin tsaro sun sanar da kama waɗanda ake zargi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumomin Haɗaka a Jihar Benuwai sun sanar da kama waɗanda ake zargi da hannu a kisan gilla da aka a yankin Yelwata dake jihar, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Kwamishinan ƴan sandan jihar, Emenari Ifeanyi ya sanar da hakan a yayin ganawa da manema labarai a ranar Lahadi, saidai bai bayyana sunayen waɗanda aka kaman ba.

Hakan ya biya bayan umarnin Shugaba Bola Tinubu na ranar Laraba ga jagororin tsaro har da Sufeton ƴan sanda na su tabbatar da kamo waɗanda suke da hannu a mummunan harin.

Lamarin da ya sa jagoran ƴan sandan ya ce za a yi nasara ne da taimakon Gwamna Hyacinth Alia na jihar.

Kwamishina Ifeanyi ya bayyana cewa, tuni jami’an da Sufeton, Kayode Egbetokun ya baza a jihar suka je wuraren da aka aika su domin tabbatar da cika aiki.

Ya kuma roƙi masu gidaje da otal-otal da su riƙa tantance waɗanda suke bai wa dakuna a wurarensu domin ƙaurace wa sake samu hari a jihar.

A makon da ya gabata ne wasu da ake zargin makiyaya ne suka farmaki al’umma a garin Yelwata dake Ƙaramar Hukumar Guma, inda suka halaka da dama da ɗaiɗaita wasu dubunnai ga barin gidajensu.

By Babaji