
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wata guguwa da ke ɗauke da tsawa a Jihar Sakkwato ta yi sanadin mutuwar mutane biyar da raunata wasu da dama a Ƙananan Hukumomin Gwadabawa da Kware.
Lamarin ya auku ne a ranar Talata, wanda Hukumomin Agajin Gaggawa na SEMA da NEMA suka tabbatar da halin damejin da al’amarin ya yi a yayin bincikensu.
A cewar binciken, tsawar ta lalata sama da gine-gine 1,400 da suka haɗa da gidajen al’umma da na gwamnati ciki har da makarantu. A Gwadabawa kaɗai, gidaje 878 ne suka rushe, lamarin da ya shafi magidanta guda 1,306 da ɗaiɗaita aƙalla 7,836.
Hukumomin sun ce, mutane 11 suka samu munanan raunuka a yayin da guda biyar ciki har da yara biyu suka rasu a ƙauyen Marabawa.
A Ƙaramar Hukumar Kware kuwa, kimanin gidaje 523 ne tsawar ta lalata, lamarin da ya shafi magidanta 1,403 da raunata mutane 18. Haka kuma ya shafi makarantu.
SEMA ta ce, za a bada takardar jaddawalin mutane da gine-ginen da al’amarin ya shafa ga gwamnatocin jihar da ta tarayya domin su tallafa musu.
