Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A wata takardar sanarwa ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Abubakar Marwana ya ce bubban daraktan hukumar Manjo Garba Yahaya Rimi mai ritaya ya faɗi haka da yake a Funtua a yayin da yake ganawa da masu ruwa da tsaki a sakatariyar ƙaramar hukumar.
Ƙungiyar masu kishin Funtua suka shirya wannan taro domin laluba hanyoyin da za a fahimci juna a tsakanin hukumar da al’ummar yankin Funtua kan wasu matsaloli da suka taso.
Manjo Rimi ya ce an kafa wannan hukuma ce domin ta tabbatar da kare lafiyar hanya da kare lafiya da dukiyar matafiya da masu ababen hawa,”haka kuma mu tabbatar masu ababen hawa sun sanya ɗa’a
a zukatan su a lokacin da suke amfani da hanya,”Rimi ya ce.
Ya ce hukumar kiyaye haɗurra na jihar Katsina da yake shugaban ci na yin bakin ƙoƙarin ta wajen ta rage yawaitar haɗurra musamman a manyan hanyoyi na jihar.
Babban daraktan ya yaba wa Gwamna Dikko Raɗɗa bisa kulawa da yake ba hukumar da hakan ya ƙarfafa musu gwiwa wajen tunkarar aikin su ba ji ba gani.
Shima da ya ke bayani wajan taron kwamandan hukumar Alhaji Dahiru Mani Bagiwa ya ce jami’an hukumar sun shirya tsaf wajen tabbatar da ganin masu ababen hawa sun bi dokokin tuƙi a hanyoyin jihar.
Daga ƙarshe masu ruwa da tsaki da suka halarci taron waɗanda suka haɗa da wakilan shugaban ƙaramar hukumar Funtua da Hakimin Funtua da wasu Dattawan yankin sun nuna jin daɗin kan yadda taron ya gudana.
Sun ce irin wannan taron shine zai kowa ƙara fahimtar juna kuma kowa ya yi abinda ya dace musamman masu ababen hawa su bi dokokin hanya , sukuma yan KASSAROTA su rinƙa wayar da kan jama’a kan bin doka kafin ɗaukar mataki.
