Basarake a Zamfara ya yi kira da a koyar da matasa sana’o’i hannu

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Sarkin Ƙaura Namoda, Sanusi Muhammad Ahmad Asha ya roƙi matasan masarautarsa da su rungumi sana’o’in kasuwanci domin su zama masu sana’ar dogaro da kai a ƙarshen karatunsu a makaranta.

Sarkin ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya ƙaddamar da horon kwana uku ga ɗalibai 167 a makarantar koyar da fasaha ta Almustaqil dake a garin Ƙaura Namoda ta shirya a yau Asabar.

A cewarsa horon ya kasance tare da haɗin gwiwar ma’aikatar ilimi ta tarayya da hukumar kula da ilimin fasaha ta ƙasa da ta amince da sabbin shirye-shiryen TVET.

“Ƙwarewar fasahar sana’oin hannu ita ce mafi kyawun hanya da za a bai wa matasanmu yayin da suke manyan makarantu domin sama wa kansu ayyukan yi a ƙarshen karatunsu.” Sarkin ya bayyana.

Ya ci gaba da cewa, a ƙarshen koyan sana’o’in, za a ba wa waɗanda suka halarci taron satifiket na haƙiƙa.

Ya shawararci hukumar makarantar Almustaqil da su bada fifiko kashi 30% a matsayin fannin karatu a cikin aji, kashi 70% a aikace ga ɗalibai don haɓaka ƙwarewar fasahar ƙirƙire ƙirƙire tsakanin ɗalibai.

Ya jaddada cewa gwamnati ita kadai ba za ta iya samar da aikin yi ga kowa da kowa ba, yana mai cewa lokaci ya yi da matasa za su canza tunanin su ta hanyar fasahar sana’oin hannu yayin da suke makaranta domin su zama masu dogaro da kai.

A nasa jawabin daraktan makarantar koyar da fasaha ta Almustaqil da ke Ƙaura Namoda Mohammed A. Nasiru Makwashi, ya bayyana cewa taken horaswar shi ne ƙarfafawa matasa gwiwa ta hanyar fasahar kere-kere da sana’o’i domin samun ci gaba mai ɗorewa.

A cewarsa, a karkashin shirin NBTE TVET Initiative Program, an amince da cibiyar ta gudanar da horon sana’o’in hannu guda goma sha biyu 12, ga ɗaliban da za su hallarci horon.

Ya ci gaba da cewa, sana’o’in da aka amince da su sun haɗa da, Kiwon kaji, ɗinki, kayayyakin abinci da gudanar da otal, sanya wutar lantarki, ayyukan kwamfuta na Social Media, walda da sauran su.

By ukarofi