Gwamna Dikko Raɗɗa ya naɗa sabbin manyan sakatarori takwas a Katsina

Spread the love

ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa, ya amince da naɗin sabbin manyan sakatarori (Permanent Secretaries) guda takwas (8) bayan ritayar wasu daga cikin manyan jami’an gwamnati.

Sabbin manyan sakatarorin sun haɗa da Yusuf Ahmed na karamar hukumar Katsina, Amina Ibrahim ita ma daga Katsina da Aishatu
Abdullahi daga Dutsinma da kuma Dasuki Ibrahim Abubakar na ƙaramar hukumar Malumfashi.

Sauran sun haɗa da Lawal Abashe daga Matazu da Ado Yahaya na Sabuwa da Sani Rabi’u na Jibiya da kuma Nasiru Ladan daga ƙaramar hukumar Kaita.

Gwamna Raɗɗa ya taya sabbin manyan sakatarorin murna tare da kira gare su da su rungumi manufofin “Gina Makomarka” ta hanyar nuna cikakken sadaukarwa wajen bauta wa jama’ar Katsina da gaskiya, jajircewa da ƙwarewa.

Ya jaddada cewa an zaɓe su ne bisa cancanta, ƙwarewa, da tarihin kyakkyawan aiki, tare da tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da yaba wa ƙwazo da kuma lada ga ma’aikatan da ke nuna biyayya da himma wajen aiki.

Za a sanar da ranar bikin rantsar da su a nan gaba.

By ukarofi