Sojoji sun ceto ƴan Chana huɗu da wasu 17 da aka yi garkuwa da su

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Dakarun sojojin Nijeriya sun yi nasarar ceto wasu mutane 21 da aka yi garkuwa da su ciki har da ƴan Chana guda huɗu yayin atisaye a jihohin Kwara da Kogi.

A wata takarda da Mataimakin Daraktan hulɗa da jama’a na riƙo na rundunar, Laftanal Kanal Polycarp Okoye, ya fitar, ya bayyana cewa an yi nasarar haka ne a ranar 17 ga watan Oktoba, 2025.

A cewarsa, dakarun shiyya ta 2 ta Birget na 12 da ke Lokoja da na Birget na 22 na Ilorin ƙarƙashin atisayen FANSAN YAMA ne suka aiwatar da atisayen.

An kafa tawagar dakarun ne da nufin fatattakar ƴan bindiga da masu garkuwa da mutane a shiyyar Arewa ta Tsakiya.

Rundunar ta ce, waɗanda aka ceto sun haɗa da maza 14, mata biyar, jariri ɗaya da ƴan Chana huɗu.

An yi nasarar ne a lokacin da jami’an suka farmaki maɓoyar ƴan ta’adda a jihohin biyu.

An ruwaito cewa wasu daga cikin mutanen da ala ceto, an riƙe su na tsawon sa da watanni huɗu.

By Babaji