Ƙungiyar Fitilar Jama’ar Bichi ta dasa bishiyoyi domin kyautata muhalli a kasuwar zamani

Spread the love

Ƙungiyar Fitilar Jama’ar Bichi ta ƙaddamar da shirin dashen bishiyoyi a kasuwar Zamani da ke cikin ƙaramar hukumar Bichi, domin inganta muhalli da samar da yanayi mai kyau ga ‘yan kasuwa da mazauna yankin.

A wajen bikin ƙaddamarwar, shugaban ƙungiyar, kuma dagacin Malikawa-Garu, Alhaji Lurwanu Idris Malikawa Garu, ya bayyana cewa shirin na cikin matakan da ƙungiyar ke ɗauka wajen tallafawa cigaban yankin. Ya ce an gudanar da dashen ne domin tallafawa ƙoƙarin ɗan majalisar tarayya, Alhaji Abubakar Kabir Abubakar, na bunƙasa kasuwar zamani ta Bichi.

“Dasa bishiyoyi zai inganta yanayi da samar da inuwa a kasuwar. Don haka muna kira ga ‘yan kasuwa da su kula da su, su riƙa basu ruwa, da kuma kare su daga lalacewa,” in ji Alhaji Lurwanu.

Shugaban kasuwar, Abubakar Muzahim Saleh, ya ce za a dasa bishiyoyi arba’in (40), inda kowace bishiya za a ba mutum ɗaya alhakin kula da ita har sai ta girma. Ya ƙara da cewa hukumar kasuwar za ta ci gaba da sa ido don tabbatar da ɗorewar shirin.

Hakimin Bichi, Galadiman Kano, Alhaji Mannir Sanusi, wanda sakatarensa Malam Idris Shitu Malikawa ya wakilce shi, ya yaba da shirin, yana mai cewa ya zo a lokacin da ake buƙatar irin wannan mataki don kare muhalli.

“Waɗannan bishiyoyi da aka dasa a daidai lokacin da ake buƙata, Allah ya taimake mu, ya kuma ba mu lafiya,” in ji shi.

Haka zalika, shugaban majalisar ƙaramar hukumar Bichi, Alhaji Hamza Sule Mai Fata , wanda shugaban kasuwar zamani, Alhaji Garba Tukur ya wakilce shi, ya tabbatar da cewa ƙaramar hukumar tana bai wa al’amuran cigaban kasuwa da muhalli cikakken goyon baya.

“Za mu ɗauki matakai don hana yara wasa da bishiyoyin domin kada su lalace, saboda haka muna kira ga jama’a su taimaka wajen ganin wannan aiki ya ɗore,” in ji shi.

Taron dashen bishiyoyin ya samu halartar jami’an hukumomi daga Hisba, NDLEA, ƴan sanda, Civil Defense,FRSC,Immigration, Fire Service, da ƙungiyoyi masu zaman kansu, ciki har da Make Bichi Green Initiative.

Malam Nasir T. Sadiq ya gabatar da jawabi kan muhimmancin dashen bishiyoyi a mahangar addini, inda ya yi nuni da cewa Al-Qur’ani mai girma ya ƙarfafa irin wannan aiki na kare muhalli da samar da alheri ga al’umma.

By ukarofi