Mashawarcin Trump, Massad Boulos ya musanta iƙirarin kisan kiyashi kan Kiristoci a Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babban mai ba Shugaba Donald Trump na Amurka shawara akan lamuran ƙasashen Larabawa da Afirka, Massad Boulos ya yi watsi da zarge-zargen cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya.

Mista Boulos ya bayyana haka ne yayin wata ziyarar aiki ga Shugaba Bola Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, ranar Juma’a.

Mashawarcin shugaban Amurkan ya faɗi haka ne yayin da ƴan majalisa a Amurka suka matsa akan kiran Fadar ‘White House’ da ta ayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ke da matsala ta musamman bisa zargin takura wa lamarin addinin Kiristoci.

Saidai, zuwa yanzu gwamnatin Trump ta yi gum akan kiraye-kirayen.

Da yake amsa tambaya game da matsayar gwamnatin Amurka akan rikicin addini a Nijeriya, babban jami’i ya ce, sanannen abu ne ga masu bibiya cewa ta’addanci “ba shi da kala, ba shi da addini sannan ba shi da ƙabila.”

Ya kuma yi tsokaci akan yadda ƴan addinai da ƙabilu suke fama da al’amarin ta’addanci, yana mai bada misali da ƙungiyoyin tsatstsauran ra’ayi kamar su Boko Haram da ISIS, waɗanda sun halaka tarin mabiya addinin Musulunci.

Ya ƙara da cewa, “mun san cewa Boko Haram da ISIS suna kashe Musulman da sun fi Kiristoci yawa. Wannan ba abu ba ne da ke harin wata tawaga ko waninta ba.”

Har’ilayau, Boulos ya ce gwamnatin Tinubu ta aiwatar da matakan tsaro da ake fatan za su bada sakamakon masu kyau yayin da ta haɗa hannu da Amurka.

By Babaji