Daga DAUDA USMAN a Legas
Shugaban Ƙungiyar Masu Sana’ar Kasuwancin Aya da Dabino a Kasuwar Mile12 da ke Jihar Legasa, Alhaji Auwalu Mai Dabino ya bi sahun ‘yan uwansa ‘yan kasuwa masu wannan sana’ar wajen ƙorafin cewa rufe shingogin tsakanin iyakar Nijeriya da Jamhuriyar Nijar ya ƙara taɓarɓara kasuwar aya da dabino a Legas.
Alhaji Auwalu ya cigaba da shaida wa Jaridar Manhaja a Legas halin da ‘yan kasuwar aya da dabino su ke ciki a Legas dangane da wannan al’amari.
Shugaban ƙungiyar ya ce, tun daga lokacin da Nijeriya ta rufe iyakokin tsakaninta da ƙasar Nijar harkokin kasuwancinsu na aya da dabino suke ta ƙara taɓarɓarewa a Legas da kewayenta gabaxaya.
Ya ƙara da cewa, aya da dabino waxansu abubuwa ne masu muhimmanci a jikinɗan Adam, kuma wani lokacin ma akan haxa waxansu magunguna da su domin zan adam ya yi amfani da shi a wajan neman samun lafiyar jikinsa
Ya cigaba da cewa, “sannan kuma aya da dabinon nan mafi yawancin su daga ƙasar Nijar ake kawo mana su a Nijeriya domin sayar wa al’umma, amma kuma sai ta kasance a halin yanz gwamnati ta rufe iyakokin tsakaninta da ƙasar Nijar.”
Ya ce, kuma Allah kaxai ya san iyakar milyoyin mutanen da suke ciyar da iyalan su da sana’ar aya da dabino a Nijeriya.
Alhaji Auwalu Mai Aya da Dabino ya ce, akan hakan yake ganin ya kamata ya baiwa Gwamnatin Nijeriya mai adalci shawara tare da tausaya wa talakawanta a wajen harkokin rayuwarsu ta yau da kullum.
Ya ce, akan hakan ya ke ƙara roƙon Gwamnatin Nijeriya da ta ƙara dubawa ta samar wa ’yan kasuwar aya da dabino mafita a game da wannan al’amari.
Ya cigaba da cewa, tun da a fahimtarsa aya da dabino ba su cikin tsarin kayan da suke da doka a wajen shigo da su Nijeriya.
Ya ce, fatan Gwamnati Nijeriya za ta share masu hawayen su dangane da wannan al’amari, sannan ya cigaba da jawo hankulan mambobin ƙungiyar ta su ta masu kasuwancin aya da dabino a Nijeriya da su cigaba da ƙasa kawunan junansu tare da sanya tsoran Allah a zukatan su a lokacin da suke gudanar da harkokin kasuwancin su na yau da kullum.
A ƙarshe, Alhaji Auwalu ya ce, yana mai taya al’ummar Nijeriya murnar cikar shekatun Nijeriya sittin da uku da samun ‘yancin kai, ya ce da fatan Allah ya cigaba da zaunar da amatsayin ƙasar nan lafiya.
