Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
An yi kira ga al’ummar jihar Kano da su gaggauta yin rajista da karɓar katin zaɓe domin tabbatar da cikakken shiga cikin harkokin dimokuraciyya da kuma zaɓen shugabanni nagari da za su inganta rayuwar jama’a.
An bayyana hakan ne yayin wani taron wayar da kai kan muhimmancin katin zaɓe da Kwamitin Wayar da Kan Al’umma kan Rajistar da Karɓar Katin Zaɓe ya gudanar a Sakatariyar ƙaramar Hukumar Bichi, tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyin aikin gayya daga ƙananan hukumomi takwas da suka haɗa da Bagwai, Bichi, Dawakin Tofa, Gwarzo, Rimin Gado, Shanono da Tsanyawa.
Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Majalisar ƙaramar Hukumar Bichi, Alhaji Hamza Sule Maifata, ya buƙaci waɗanda har yanzu ba su yi rajistar katin zaɓe ba da su yi amfani da damar da ta rage kafin ranar 10 ga Yuli, wadda aka tsara a matsayin ranar kammala aikin rajistar.
Ya ce ƙaramar hukumar na ci gaba da ɗaukar matakan tabbatar da cewa kowane mai haƙƙin zaɓe ya mallaki katinsa, tare da yabawa gudunmawar shugabannin yankin, musamman ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Bichi, Alhaji Abubakar Kabir Abubakar, da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin.
“Ko wane hali mutum yake ciki, katin zaɓe na da muhimmanci. Ta hanyar ƙuri’arka ne za ka zaɓi wanda kake so ya jagorance ka ko kuma ka sauya wanda bai cika maka buri ba,” inji Maifata.
Shi ma ɗaya daga cikin mambobin kwamitin, Malam Usman Bello, ya yi bayani kan matakan rajistar katin zaɓe, inda ya bayyana cewa akwai sabbin masu rajista, masu gyaran bayanai ko maye gurbin katin da ya lalace, da kuma waɗanda suka sauya mazaunin zaɓe.
Ya kuma ƙarfafa gwiwar jama’a da su fara cike bayanansu ta yanar gizo kafin zuwa ofisoshin Hukumar Zaɓe domin sauƙaƙa aikin tantancewa da ɗaukar bayanan yatsu.
A nasa jawabin, Kwamishinan ƙananan Hukumomi da Masarautu na Jihar Kano, Alhaji Tajo Muhammad Othman, wanda Mataimaki na Musamman ga Gwamna kan Wayar da Kai daga Matakin ƙasa, Alhaji Isma’il Shehu Gurjiya ya wakilta, ya ce ziyarar na gudana ne bisa umarnin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf.
Ya bayyana cewa ƙaramar Hukumar Bichi ce ke kan gaba a jihar wajen yawan mutanen da suka karɓi katin zaɓensu, lamarin da ya nuna yadda al’ummar yankin suka fahimci muhimmancin shiga cikin harkokin zaɓe.
Gurjiya ya ce katin zaɓe na taka muhimmiyar rawa wajen tsara manufofin gwamnati da suka shafi tattalin arziki, ilimi, noma, tsaro da sauran fannoni na rayuwar al’umma.
Taron ya samu halartar shugabannin ƙananan hukumomi, daraktoci, shugabannin sassa, jami’an gwamnati, ƙungiyoyin farar hula, mata, matasa da sauran masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na jihar.
