Keyamo ya yi ƙarar EFCC da ICPC a kotu, ya nemi su tuhumi Atiku

Daga AMINA YUSUF ALI

Festus Keyamo, mai magana da yawun majalisar kamfe ta jam’iyyar APC, ya shigar da ƙara a kan hukumar hana cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), yana neman kotu ta kama Atiku Abubakar, ɗan takarar jam’iyyar PDP na shugabancin Nijeriya.

A cikin ƙarar, Festus Keyamo wanda lauya ne mai muƙamin SAN ya haɗa da dokar Hukumar daƙile laifukan cin hanci da makamantansu (ICPC) Hukumar kula da dokar ɗa’ar aiki (CCB) a cikin ƙarar, bayan wa’adin awoyi 72 da ya bayar sun cika.

Keyamo, lauya mai muƙamin SAN, ya ba da wa’adin ne a cikin wata wasiqa wacce ya aike ranar 16 ga watan Janairu, 2023, inda ya yi nufin aike ta ga Shugabannin hukumomin EFCC, ICPC da kuma CBC.

A cikin wasiƙar gargaɗin, ya nemi da hukumomin lallai su gurfanar da Atiku a kan laifukan da ake zarginsa na sava wa dokar ɗa’a ta mulkin al’umma, badaƙalar kuɗaɗe, cin amanar al’umma da kuma haɗin baki wajen aikata laifi.

Keyamo ya yi wannan kira ne bayan da ya kalli bidiyon da tsohon mataimakin Atiku, Michael Achimugu, ya saki.

A cikin bidiyon wanda aka saki makwanni kaɗan da suka gabata, Achimugu ya yi tonon silili kala-kala a game da laifukan ɗan takarar shugaban ƙasar na PDP ya aikata.

Ya yi ikirarin cewa, tsakanin shekarar 1999 da 2007 lokacin da Atiku yana Mataimakin Shugaban ƙasa, ya haɗa kai da tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo wajen tatike ƙasar nan ta hanyar abinda ya ambata da “Ababen hawa na Musamman” (SPVs).

A kan wannan ne Keyamo ya nemi Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja da ta tilasta wa hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa na ƙasar nan da su yi zurfafaffen bincike a kan al’amarin, kuma su gurfanar da Atiku.