Samar da maƙabartar Kiristoci a Bauchi: Gwamnati ta buƙaci jama’a su kai zuciya nesa

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Gwamnatin Jihar Bauchi ta buƙaci al’ummomin Musulmi da na Kiristoci mazauna unguwannin Yolan Bayara dake cikin gundumar Miri ta Ƙaramar Hukumar da su riƙa kai wa zukatunsu nesa da zummar wanzar da zaman lafiya, mutunta juna, yakana, tare da shure bambance-bambance dake a tsakanin domin nusar da cigaban jiha da ƙasa baki ɗaya.

Mai bai wa gwamnan jiha shawarwari akan kafofin watsa labarai da yayatawa, Mukhtar Gidado Mohammed shine ya gabatar da wannan buƙata ta gwamnatin jiha dangane da taƙaddama dake gudana a tsakanin al’ummomin guda biyu, yana mai cewar, filin maƙabarta da ake taƙaddama akan sa, har ya zuwa wannan lokaci ba a bayar da shi wa wani maluƙi ko ƙungiya ba.

Alhaji Mukhtar Gidado Mohammed yana mayar da martani ne bisa koke da al’ummar Musulmi mazauna Yolan-Bayara suka yi a kwanakin baya dangane da wannan lamari, yana mai cewar, gwamnati takan bayar da filin ƙasa ne bisa buƙatar da ta shallace son zuciyar jama’a.

Gidado ya ce: “Hankalinmu a matsayin gwamnati ya hankalta da wani taron manema labarai da Ƙungiyar Al’ummar Musulmi mazauna gundumar Yolan-Bayara dake bayan Babban Asibitin Bayara suka yi yau a nan Bauchi. Abinda ke faruwa shine, Ƙungiyar Mabiya Addninin Kiristanci (CAN) ta rubuta wa gwamnati takarda tare da koken buƙatar a ba su wani ɗan fili da za su mayar da shi maƙabartar mabiya addininsu a nan yankin Bayara dake cikin da’irar garin Bauchi.”

Mai bai wa gwamna shawarwari ya ce, “gwamnatin jiha ta bayar da umarnin a duba wani fili a nan farfajiyar waɗannan al’ummai mai kimanin kadada hamsin bisa dubi da cancantar a bai wa masu waɗannan buqata bayan bibiyar dukkan ƙa’idoji na doka da suka dace da yin hakan, daga cikin babban filin da yake da murabba’in kadada 470 dake cikin wannan yanki na mazaunar waɗannan al’ummai.

“Dangane da nazarce-nazarce da suka jiɓanci bayar da wannan fili da ake buƙata, ya sa gwamnatin jiha ta kafa wani kwamiti a ƙarƙashin jagorancin Muƙaddashin Gwamna, Sanata Baba Salihu Tela, haɗi da wani ƙwararre a kan lamuran yin amfani da fili da safiyon sa, waɗanda za su yi nazarin bayar da filin ga mabuƙata.”

Kamar yadda mai magana ya ce, kwamitin da aka kafa zai yi nazarin duba wannan fili da ake buƙata, tare da shawartar gwamnati bisa yin abinda ya dace, yana mai cewa, “Yayin da Muƙaddashin Gwamna da ‘yan kwamitin suke nazartar wannan lamari, sai kwatsam al’ummar Musulmi na wannan gunduma suka rubuta wa gwamnati takardar koke da nunin cewa wannan fili na tasu al’umma ce.

“Wannan fili da ake yin husuma akan sa, har zuwa wannan lokaci ba a bayar dabshi wa kowa ba, domin har yanzu gwamnati tana cikin yin nazarin duba ƙa’idojin bayar da shi, kuma wajibi ne jama’a su san cewa a duk wani yanayi da gwamnati za ta bayar da filin ƙasa, walau wa ɗaiɗaikun jama’a ne ko ƙungiyoyi, takan yi dubi da ƙa’idoji ne kamar yadda dokar fili ta zayyana, tare da yin nazarin diyya da ya kamata a bai wa masu mallakar filin idan ya kasance na ɗaiɗaikun jama’a ne ko al’umma.”

Mai bayar da shawara wa gwamna ya bayyana cewar, dukkan al’umman guda biyu, Musulmi da Kiristoci suna da ‘yancin neman fili daga wajen gwamnati domin buƙatar samar da maƙabarta, kuma gwamnati a bisa irin hali nata na mutunta mai rai da mamaci, irin gwamnatin Gwamna Bala Mohammed mai ƙarfafa zukata, takan yi amfani da nata damar bisa bin qa’idojin doka ta bayar da fili ko filaye wa kowace al’umma bisa bin tsari da ya kamata.

Mashawarci Mukhtar Gidado ya ce, “don haka a wannan hali ko yanayi, kamar yadda ta saba, za ta mutunta kowane addini ko al’umma da zummar yin adalci, salama da zaman lafiya. Wannan shine matsayar dangane da wannan batu.”

Gidado daga nan sai ya yi kira da kakkausar murya wa manema labarai da wajibi ne a yayin tsara labaran su su yi kaffa-kaffa da kuma yin amfani da ƙa’idojin gudanar da ayyukansu a dukkan lamura, musamman waɗanda suka jivanci lamuran addini ko siyasa, husasan a wannan lokaci da al’ummar Nijeriya take tunkarar zaɓen gamagari.

Gidado ya nanata cewar, wajibi ne wa manema labarai suyi aiki da dukkan ƙa’idojin gudanar da ayyukansu, na bibiyar shimfiɗaɗɗun ƙa’idojin gudanar da ayyukan aikin jarida, musamman dangane da lamura da suka jiɓanci addini da hauma-haumar siyasa, wajibine a gudanar da ayyyuka cikin zaman lafiya da salama.

Wannan taƙaddama dai ta taso ne makon da ya gabata, lokacin da al’ummar musulmi mazauna Yolan-Bayara suka gudana da wani taron manema labarai, inda suka nuna rashin gamsuwar su bisa filin maƙabarta da suke kyautata zaton an bai wa al’ummar mabiya addinin Kirista, suna masu cewar, wannan fili da aka bayar na kakanin-kakaninsu ne.

Tawagar ta al’ummar Musulmi na Yolan Bayara ta gudanar da taron manema labaran ne a ƙarƙashin jagorancin Sani Sarki Yakubu wanda ya bayyana cewar, filin da suke yin magana akai na iyaye da kakanin sune wanda a tuntuni ya kasance makabarta ce ta al’ummar Musulmi, wanda har ya zuwa wannan lokaci nanne suke bunne mamatan su, don haka idan ya sake kasance wa makabartar mabiya addinin Kiristanci, zai kasance ana tone mamatan Musulmi, ana musanyawa da mamatan ma’abutan wani addini, suna ganin yin hakan ba zai daɗaɗa wa kowane jinsin addini ba.

Malam Sani Yakubu ya kuma bayyana cewar, wasu daga cikin mamatansu dake kwance a maƙabartar a yanzu haka bisa karamar Ubangiji idan za a tone, za a same su garau tamkar barci suke yi, ya ce wannan karama ce da Allah yake yi wa wasu bayinSa.

Yakubu ya bayyana cewar, su al’ummar Musulmi mazauna Yolan Bayara basu yin wata tababa ko baqin ciki na al’ummar mabiya addinin kiristanci su samu makabarta, domin dole ne mamaci a turbuɗe shi a cikin ƙasa, walau Musulmi ko Kirista, amma akwai filaye bargaje a sassan kewayen garin Bauchi inda za’a iya musanyawa da filin da ake taƙaddama akan sa, da zummar zaman lafiya tsakanin al’ummai daban-daban dake cikin ɗaukacin jihar nan.

“Su Kiristoci, ‘yan uwan mu ne maza da mata, kuma tare muke zaune shekaru aru-aru cikin kwanciyar hankali da lumana a tsakanin mu, don haka ba mu ƙaunar wani saɓani ya wanzu a tsakanin mu. Kuma mu masu biyayya ne wa gwamnati, kuma masu bin doka”, inji jagora Sani Yakubu.

Yakubu ya ce, “idan gwamnati ta ce a yanzu ta ba su wannan maƙabarta, muna sanar da Mai Girma Gwamna akwai iyayen mu da kakanin mu da suke kwance a wajen domin gidaje ne ko’ina, kuma a gida ake biso, kuma yanzu idan ya zama makabarta, dole za’a je ana tono, wata rana kuma za’a tono wani bawan Allah wanda yana kwance har yanzu jikinsa bai canja ba. Kuma kaga Musulmi yanzu ba zai samu wani dama da zai kai ziyara yayi addu’a wa iyayensa da kakanni da suke kwance a wajen ba”.

Ya ƙara da cewar: “Ba mu cewa, mu, munfi ƙarfin gwamnati, muna ƙarƙashin gwamnati ne, amma muna sanar da gwamnati domin muma tayi mana adalci, domin Kiristoci ‘yan-uwan mune, muna zaman lafiya dasu, bamu son abinda zai kawo mana tashin hankali a tsakaninmu.”