Masarautar Katsina ta tuɓe Makamanta, Sule Idris

Daga BASHIR ISAH

Masarautar Katsina a Jihar Katsina, ta tuɓe Alh. Idris Sule Idris a matsayin Makaman Makamanta.

Sanarwar haka na ƙunshe ne cikin wasiƙar da masarautar ta aike wa basaraken mai ɗauke da lamba KEC/O12/BKRLG/NOL.III/87 da kuma kwanan wata 19 ga Janairu, 2023.

Wasiƙar wadda ta samu sa hannun Wakilin Sarki kuma Ƙauran Katsina, Alh. Aminu Nuhu Abdulkadir, ta nuna Masarautar ta ɗauki wannan mataki ne saboda ƙorafe-ƙorafen da aka samu a kan wanda lamarin ya shafa.

A cewar wasiƙar, “Bisa ga takardar da Majalisar Mai Martaba Sarkin Katsina, Alh. Dr Abdulmumini Kabir Usman CFR, ta samu daga Ofishin Gwamnati mai lamba SEC/54/VOLVI/1416 ta ranar 18/1/2023.

“Wadda Maigirma Gwamnan Jiha ya tabbatar da ƙorafe-ƙorafen da ya samu, kuma da aka bincika kana da masaniya a kansu, wanda ya kawo rashin zaman lafiya a ƙasarka.

“Don haka, Masarautar Katsina ta yanke shawarar sallamarka daga sarautar Makaman Katsina daga yau Alhamis 19/1/2023,” in ji wasiƙar.