Gwamnatin Nijeriya ta amince da Naira tiriliyan 1.9 don aikin gina hanyoyi 44

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar Zartaswa ta Tarayya a ranar Laraba, ta amince da shawarar da ma’aikatar ayyuka da gidaje ta bayar na ganin kamfanin mai na ƙasa NNPC ya zuba kuɗi Naira tiriliyan 1.9 don aikin sake gyara hanyoyi 44 a faɗin Nijeriya.

Mataimaki na musamman kan harkokin yaɗa labaru a ofishin mataimakin shugaban ƙasa, Laolu Akande, shi ya sanar da haka bayan taron da mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta.

Akande ya ce kuɗaɗen da ake sa ran kashewa sun kasance don ci gaba da aiwatar da tsarin bunƙasa ababen more rayuwa ne na tituna da kuma gyara tsarin bada harajin zuba jari na gwamnatin tarayya, kashi na biyu na NNPC Ltd da sauran rassansa.

Ya ce majalisar ta kuma amince da masu bada kwangilar gina tituna guda tara a ƙarƙashin tsarin gwaji na shirin bunƙasa manyan tituna da gudanar da ayyukansu bayan bayar da cikakken takardar shaidar bin ƙa’idojin kasuwanci da hukumar kula da hanyoyin samar da ababen more rayuwa ta yi na tsawon shekaru 25.

Aikin hanyoyi da aka amince a matakin farko sun haɗa da hanyar Benin-Asaba da Abuja-Lokoja-Onitsha-Owerri-Aba-
Shagamu Benin da Abuja-Keffi-Akwanga-Lafia da Makurdi da hanyar Kano-Maiduguri da hanyar Enugu-Port Harcourt da Legas-Ota-Abeokuta da kuma Legas-Badagry zuwa Seme.