Shirin Bankin Access na mallakar Bankin Sidian ya gamu da tazgaro

Daga AMINA YUSUF ALI

A yanzu haka dai yunƙurin da bankin Access yake yi na ƙoƙarin mallakar Bankin Sidian wanda babbar shalkwatarsa take a jihar Kenya ya haɗu da tazgaro, inji Bankin na Access a ranar Alhamis ɗin makon da ya gabata.

Bankin ya ƙara da cewa, Wannan yarjejeniyar cinikayyar da aka ƙulla kusan watanni shida da suka wuce da za ta ba shi damar mallakar Bankin Sidian ɗin ta rushe. Don haka, ba za a cigaba da maganar ba.

Bankin Access ya yi niyyar sayen kaso 83.4 na Banki Sidian da yake a Afirka ta Yamma. Tun a farkon watan Yunin shekarar 2022 da ta gabata aka fara zancen kuma ana sa ran zai tabbata. Sai dai abin kuma ya zo ya rushe.

Bankin Sidian dai mallakin kamfanin zuba jari na Centum Investment Company na ƙasar Kenya ne, wanda ya amince da sayarwar a kan Dalar Amurka miliyan $37.

Sai dai kuma saboda rashin cikar wasu sharruɗɗan na yarjejeniyar, ya sa abin ya kasa yiwuwa. Amma wataƙila a nan gaba idan sharruɗɗan suka cika, za a iya sasantawa, a cewar Bankin Access.