
Daga BELLO A. BABAJI
Rundunar ƴan sanda a Jihar Kogi ta tabbatar da mutuwar wani manjon soja mai ritaya mai suna Joe Ajayi a hannun waɗanda suka yi garkuwa da shi bayan sun amshi Naira miliyan 10 daga wajen iyalansa domin a sako shi.
Kakakin rundunar, SP Williams Ovye-Aya ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai (NAN) a Lokoja, ranar Litinin.
NAN ya ruwaito cewa, an yi garkuwa da Ajayi, mai shekaru 76 ne a gidansa dake Odo-Ape, a Ƙaramar Hukumar Kabba-Bunu a jihar, ranar 21 ga watan Mayu.
Kakakin ƴan sandan ya ce, an gano gawar mamacin tare da kai ta Asibitin Specialist a Kabba a inda aka ajiye ta a ɗakin ajiyar gawawwaki.
Rundunar da tabbatar da cewa lallai za a farauto masu hannu a aikata laifin tare da gurfanar da su domin su fuskanci hukuncin doka.
Haka kuma Shugaba da Sakataren ƙungiyar ‘Bunu Leaders Forum’, Farfesa Olu Obafemi da Dakta Ade Abanida sun tabbatar da aukuwar al’amarin.
Sun ce, da fari ƴan bindigar sun buƙaci a biya su miliyan N50 ne, wanda iyalansa suka gaza biya, inda daga nan rashin lafiyar marigayin ya fara tsanani saboda babu kulawa a tare da shi.
Ganin haka ya sa ƴan bindigar suka rage kuɗin fansar zuwa Naira miliyan 10, wanda bayan sun biya ne sai ƴan bindigar suka faɗa musu wajen da za su same shi. Daga nan aka je wajen, inda aka same shi babu rai.
