
Daga BELLO A. BABAJI
Jam’iyyar APC ta yi gargaɗi ga tsohon mai tsawatarwa a Majalisar Dattawa, Sanata Ali Ndume, bisa kalamansa na cewa akwai yiwuwar irin yadda tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Johnathan ya gaza koma wa mulki a karo na biyu, ya faru da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Ta ce, duk da cewa tana maraba da ra’ayoyi mabanbanta, haka kuma tana da hanyoyin ladabtar da mambobinta da suka saɓa wa dokokinta.
A wata hira da Daraktan yaɗa labaranta, Bala Ibrahim ya yi da manema labarai a ranar Litinin, ya ce APC jam’iyya ce da ke karɓar ra’ayoyi da dama ba tare da kawo tsaiko ba.
A ranar Lahadi ne Ndume ya bayyana kalaman nasa ta gidan talabijin na Channels, inda ya ce matuƙar Tinubu bai ɗauki darasi ba daga faɗuwar Johnathan a zaɓen 2015 ba, akwai yiwuwar shi ma ya rasa nasara a zaɓen 2027.
A shekara 2015 ne Jonathan, wanda shi ne Shugaban ƙasa a lokacin, ya rasa damar koma wa kujerar bayan da Muhammadu Buhari na APC ya doke shi.
Buhari ya samu ƙuri’u 15,424,921, a yayin da Johnathan ya zo na biyu da ƙuri’u 12,853,162.
Lamarin da ya sa a karon fari a tarihin Nijeriya aka samu shugaba mai mulkin da ya rasa damar komawa a karo na biyu.
