Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wata Kotun Majistare a Kano da ke zamanta a unguwar No-man’s-land a Sabon Gari, ta bayar da umarnin a tsare wani mai shagon saida magani (Chemist) a gidan yari bisa zargin yi wa wata yarinya ‘yar shekara tara fyaɗe.
Lauyan jiha, Barista Zainab Aliko, ta shaida wa kotun cewa, ana tuhumar mai shagon saida maganin, Manniru Ibrahim Fanisau da yi wa marigayiyar, Rumaisa Sadik fyaɗe, a lokacin da aka kawo masa ya duba ta saboda tana fama da Maleriya.
Barista Aliko ta ƙara da cewa a sakamakon lamarin yarinyar ta mutu.
Wanda ake tuhumar ya ƙi amsa laifuka biyun da ake tuhumarsa da su na fyaɗe da kisan kai da suka saɓa da sashe na 283 da 221 na dokar laifuka ta jiha.
Alƙaliyar kotun, Hajara Safiyyu Garba, ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake zargi a gidan gyaran hali.
Garba ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 30 ga Satumba, 2024.
