Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wata Kotun Majistiri da ke jihar Sakkwato a ranar Laraba ta bada belin Shafi’u Umar, hadimin tsohon Gwamnan jihar, Aminu Tambuwal, kan Naira miliyan ɗaya.
Shafi’u Umar mai shekaru 37, ana zarginsa da yaɗa ƙarya kan Gwamna Ahmad Aliyu da matarsa a shafin sada zumunta na zamani.
Haka kuma ana tuhumar sa da ɓata suna.
A ranar 26 ga watan Agusta ne aka fara shari’ar, inda ɗan sanda dake gabatar da ƙara, Sufeto Abdulrahman Mansur, ya ce laifin ya saɓa da dokar Panel Code.
A cewar takardar rahoton farko, wanda ake ƙarar ya aikata laifin ne a ranar 18 ga watan Yuli.
Takardar tuhuma ta ce wanda ake ƙarar, ya yaɗa bidiyon matar gwamnan, Fatima Aliyu tana “liƙa” kuɗi a yayin bikin tunawa da ranar haihuwar ta a yayin da ake fama da matsin tattalin arziki a jihar.
Haka kuma an zargi Shafi’u Umar da wallafa takardun makaranta dake nuna Gwamna Aliyu ya faɗi jarrabawar Turanci da kuma gazawar sa wajen iya harshen na Turanci.
Wanda ake zargi ya musanta aikata laifin inda aka tura shi gidan kurkuku.
