Ranar 12 ga Rabi’ul Auwal ta shekarar Musulunci ce ranar da al’ummar Musulmi a faɗin duniya ke murnar haihuwar fiyayyen halitta, Manzon Allah salallahu alaihi wa sallam. Watan Rabi’ul Auwal shine wata na uku a kalandar Musulunci.
A Nijeriya, kamar yawancin ƙasashe, Gwamnatin Tarayya ta sanya ranar Mauludi a matsayin ranar hutun aiki. Tun kafin ranar ma al’ummar Musulmi suka fara bukukuwan shigowar watan na Mauludi, kuma za su ci gaba da yi har zuwa ƙarshen wata ko ma bayan hakan, kamar yadda wasu ke yin taren wata da rakiyar wata. Wato taren wata shine fara bukukuwan Mauludi kafin gabanin shigowar watan Rabi’ul Auwal, rakiyar wata kuma shine ci gaba da bukukuwan Mauludi bayan watan ya fita.
A lokacin gudanar da wannan daɗaɗɗen bikin murnar, ana gudanar da waƙoƙin bege na yabon Manzon Allah (SAW) tare da yin karatu da addu’o’i. Ana kuma yin girke-girke da yanke-yanken dabbobi da kaji da tattabaru da sauran kayan nama baya ga kayan shan daban-daban da ake rabawa a guraren waɗannan bukukuwa. Ana saka ƙananan yara su yi harda a makarantun islamiyya, don yin tulawarsu a lokacin bikin. Mauludi dai biki ne mai cike da farin ciki da annashuwa.
An haifi Manzon Allah Annabi Muhammadu sallahu alihi wa sallam a birnin Makka da ke ƙasar Saudiyya a shekara ta 571 bayan rasuwar Annabi Isa. Allah ya aiko masa da manzanci ne a lokacin da ya ke ibadar kaɗaici a Kogon Hira da ke bayan garin Makka. Ya fara kira zuwa ga Musulunci ne ga al’ummarsa ta ƙuraishawa a Makka, inda da fari suka ƙyamace shi, domin hakan ya yi karo da koyarwar addinin da suke yi na bautar gumaka.
Sun azabatar da shi tare da yin iyaka bakin ƙoƙarinsu wajen ganin sun kashe ‘sabon’ addinin da ya zo da shi, amma jajircewar Manzon Allah (SAW) da goyon bayan da ya samu daga iyalinsa da sahabbansa da kuma uwa-uba Allah ubangijin talikai, hakan ya taimaka masa wajen samun galaba.
Canji ya zo ne ga addinin Islama tare da bunƙasarsa bayan da ya yi hijira zuwa birnin Yathrib, wanda a yanzu ake kira da Madina, inda a nan ne aka yi masa kyakkyawar tarba. Al’amarin ya faru ne a shekarar da ya yi ƙaura zuwa Madina, wacce da ita ake lissafin shekarar Musulunci kuma hakan ne ya tabbatar da Musulunci a matsayin karɓaɓɓen addini a duniya.
An yi yaƙe-yaƙe tsakanin tsakanin kafiran Makka da waɗanda suka yi imani da addinin da Muhammadu (SAW) ya zo da shi, kuma Musulunci ya samu gagarumar nasarar da ta kai ga kafa daular Islama a yankin gabaɗayan Peninsula na Larabawa har zuwa nahiyoyin Afrika, Asiya da Turai shekaru da dama bayan wafatin Manzon Allah (SAW).
Musulunci shine addini na biyu mafi yawan mabiya a duniya bayan Kiristanci, amma a yanzu Musulunci ne addini na ɗaya a mafi yawan samun ƙarin mabiya a duniya bakiɗaya.
Akwai ɗariƙu daban-daban a cikin Musulunci a kowacce nahiya. A yanzu yawan al’ummar Musulmi ya kai biliyan 1.907, wanda ya fi kashi 25 cikin 100 na mutanen duniya bakiɗaya.
Sai dai kuma wani abin takaici a duniyar yanzu shine, wasu ƙalilan daga cikin mabiyan addinin Musulunci sun yi nasarar ɓata masa suna ta hanyar yi masa fenti da ayyukan ta’addanci, wanda ya haɗa da kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba da haifar da asarar dukiyoyi da gine-gine. Wannan ya buɗe ƙofa ga maƙiya Musulunci wajen fakewa da hakan, don shafa masa kashin kaji, musamman a kafafen yaɗa labarai.
Ainihin saƙon da Musulunci ya ke yaɗawa shine, zaman lafiya da ƙaunar juna. Hatta ita kanta kalmar Musulunci ma’anarta shine, zaman lafiya. Annabi Muhammadu (SAW) yana wa’azi ne da mutane su kasance masu haƙuri da juriya da zaman lumana da kuma ƙaunar juna. Shi ma Allah da kansa Mai Jinƙai da Yafiya ne.
Haƙiƙanin saƙon Musulunci, wanda shine ya ke ci gaba da yaɗuwa duk da ƙoƙarin da wasu ke yi na yin ƙafar ungulu ga hakan, ya haɗa da haɗa kai tsakanin Musulmi da waɗanda ba Musulmi ba, kamar yadda aka gani a tarihin rayuwar Manzon Allah Muhammadu (SAW). Wannan koyarwar ita ce tushen abin da ake karantarwa a lokacin bukukuwan Mauludi.
Tunawa da ranar haihuwar Manzo (SAW) ya haɗa da tunawa da yadda ya rayu. Musulmi su na bukukuwan ne ta hanyar haɗuwa waje guda kan soyayyarsa da saƙon da ya kawo wa bil adama da kuma cuɗayya tsakanin mabambanta addinai.
Don haka, mu a Blueprint Manhaja mun fahimci wannan daraja ta ɗan adam da ke ƙunshe cikin saƙon, shi ya sa mu ke kira ga dukkan al’ummar Musulmi da su yaɗa wannan saƙo na Musulunci kuma su yi koyi da koyarwar. Ya kamata Musulmi su yi amfani da wannan dama wajen inganta imaninsu da kyautata wa al’umma, musamman tushen ɗabbaƙa zaman lafiya tsakanin Musulmi da waɗanda ba Musulmi ba.
A ƙasa, wacce ta ke ƙunshe da mabambantan addinai, kamar Nijeriya, mu na buƙatar ƙauna da fahimtar juna, maimakon nuna bambanci a tsakanin mabiya addinai daban-daban a ƙasar tare da ƙoƙarin gina ƙasar da za mu yi alfahari da ita. Hakan zai sanya bikin Mauludi ya zamto abin alfahari ba wai kaiwai ga Musulmi kaɗai ba, har ma ga dukkan ’yan Nijeriya.
