Tinubu na shirin yi wa ministoci garanbawul

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Alamu masu ƙarfi na nuni da cewa, Shugaba ƙasa Bola Ahmed Tinubu na shirin aiwatar da wani babban garanbawul a gwamnatinsa ta hanyar yin manyan sauye-sauye ga ministocinsa, inda har ake kyautata tsammanin zai iya rushe Ma’aikatar Harkokin Jinƙai da Agaji.

Wannan dai na ɗaya daga cikin abubuwan da ake tsammanin shugaban ƙasar zai yi idan ya tashi garambawul a Majalisar Zartaswa ta gwamnatinsa ne.

Har ila yau, garambawul ɗin zai dunƙule wasu ma’aikatu da hukumomi wuri guda, yayin da wasu ministoci za a sauke su daga muƙamansu, kamar yadda wata majiya daga Fadar Shugaban ƙasa ta shaida wa Blueprint Manhaja.

Tinubu dai na fuskantar matsin lamba daga ciki da wajen jam’iyyarsa ta APC na korar ministocin da ba su taɓuka abin kirki ba a majalisar ministocinsa.

Duk da cewa, shugaban ƙasar ya yi gargaɗi game da rashin aikin yi kimanin watanni 10 da suka gabata, majalisar ministocin ta ci gaba da kasancewa cikin kwanciyar hankali, idan ban da dakatar da Ministar Harkokin Jinƙai da Agaji, Dr. Betta Edu, ba.

A watan Nuwamban da ya gabata, bayan wani taro na kwanaki uku da mambobin majalisar ministoci da hadiman shugaban kasa suka yi, Tinubu ya sanar da cewa, sashen bayar da agaji na tsakiya ƙarƙashin jagorancin mai ba shugaban ƙasa shawara ta musamman kan harkokin siyasa, Hadiza Bala-Usman, za ta auna ayyukan ministoci da sauran manyan jami’an gwamnati.

Ayyukansu shine zai tantance wanda za a bari, da kuma wanda za a kora, inji Tinubu.

Wani jami’an gwamnati da ya nemi a sakaya sunansa ya ce da yiwuwar a rushe ma’aikatar jin ƙai bayan dakatar da Dr. Betta Edu tun a watan Janairu.

“Ina tunanin an ƙara samun jinkiri, hasali ma a makon jiya ya kamata Tinubu ya sanar da sauye-sauyen to amma ba ya ƙasar.

“Bari na faɗa maku wani abu, shugaban ƙasa na iya rusa ma’aikatar jinƙai, saboda yana ganin babu buƙatar ta a yanzu, akwai hukumomin da suke aikin da take yi,” inji majiyar.

By ukarofi