Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Mai martaba Sarkin Katsina Abdulmummuni Kabir Usman zai naɗa mataimakin gwamnan jihar Katsina Lawal Farouk Joɓe a matsayin Sarkin Fulanin Joɓe.
Haka kuma shi ma shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Katsina Alhaji Jabiru Tsauri za a naɗa shi a matsayin Lamiɗon Katsina.
Har-wa-yau duk rana guda Sarkin zai naɗa shugaban kwamitin harkokin cikin gida na majalisar wakilai mai wakiltar Musawa da Matazu Alhaji Abdullahi Aliyu a matsayin Dujuman Katsina.
Tuni dai Gwamna Dikko Raɗɗa ya ɗauki nauyin gayyatar jama’a wajen naɗin sarautun da ya bayyana a matsayin abin tarihi a gare shi.
Da yake hira da manema labarai akan naɗin sarautun ya bayyana waɗanda za a naɗa a matsayin mutane ƙwararru ga gaskiya da riƙon amana domin a cewarsa ya yi aiki da su.
“Tunda nasan Dujuman Katsina shekaru 40 da suka wuce yana matashi mutum ne mai alheri da son ganin ya yi wa kowa daidai,” Dikko Radda ya faɗi haka.
Da ya juya akan Lamiɗon Katsina kuwa, gwamnan ya ce tarayya sa da shi kuwa shi ma ƙauna ce da jajircewa wajan tafiyar aikinsa ya sa ya cigaba da aiki da shi a matsayin shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin.
Malam Dikko Raɗɗa ya ƙara da cewa kasancewar Jabiru Tsauri a matsayin shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin ya sa hankalinsa a kwance wajen tafiyar da harkokin gwamnatin na.
Akan mataimakinsa kuwa Farouk Lawal Joɓe ya ce bai yi nadamar zaɓarsa a matsayin mataimakinsa ba duba da yadda yake tafiyar da harkan gwamnati.
Gwamnan ya bayyana cewa duk gwamnan da ya samu mataimaki irin Joɓe to ya yi sa’a.
“Mutum ne da yasan abinda yake yi kuma duk goyon bayan da ake nema a harkar tafiyar gwamnati yana badawa ga jajircewa wajen ganin komai ya tafi daidai,” gwamnan ya ce.
“Har na tafi hutu na wata guda a ƙasar waje kaman ina nan domin tun da na tafi ina biyar sa har nadawo kamar ban tafi ba domin babu abinda ya canza,” Dikko ya ce.
