Aikin CRC: Burina Fagge ta zama akan gaba – Hon. Habu Fagge

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano 

Shugaban Hukumar CRC mai kyautata ɗa’a, ilimi da tarbiyyar al’umma da aka fi sani da CRC  Community Re-orrientation Council wacce manyan ayyukanta akwai aikin bunƙasa ilimi ta hanyar gyaran makaratun firamare na jihar Kano, wanda kowacce ƙaramar hukuma za ta samu gyaran makaratun aƙalla biyar da CRC za ta yi kafin shigowar sabuwar shekarar 2025 in Ubangi ya amince, kamar dai yadda hukumar CRC a matakin jihar Kano ta tabbatar a wannan lokaci.                         

Hon. Alhaji Habu Muhammad Fagge, shi ne shugaban CRC na ƙaramar hukumar Fagge a Kano, ya faɗa a hira da manema labarai cewa su ma hukumar CRC ta jihar Kano gyara makarantu biyar ta ba Fagge ta gyaran amma, su makarantu shida za su gyara a ƙaramar hukumar Fagge sakamakon ganin wata makaranta da ke tsananin buƙatar a gyara kamar yadda Hon. Alhaji Habu Muhammad Fagge, shugaban CRC na Fagge kuma shugaban kula da hukumar fansho ta jihar Kano ya bayyana a wannan makon.                                      

Har ila yau Fagge ya ce koda yake zanga-zangar ƙuncin rayuwar da matasan Nijeriya suka yi ta kawo wa aikin cikas na rashin kammaluwarsa kamar yadda a ƙarshen shekarar zangon karatu na 2024 wanda hakan ta sa suka ninka yawan ma’akatan wannan aiki na gyaran makarantun shidan da CRC ta Faggen ke yi don gaggauta kammala wanan aiki cikin ƙanƙani lokaci a matakin farko a ƙaramar hukomar Fagge.   

Hon Alhaji Habu Muhammad Fagge ya ce mataki da CRC ta Fagge ta ɗauka na gyara makaranta guda da ingancin aikinsu na sa ran za su zama na ɗaya ko na biyu a tsakanin ƙananan hukumomin jihar Kano 44 da CRC ke gyaran makaratun firamaren Kano. Kuma aikin CRC babban burina mu samu taimakon Ubangiji da abokan aiki da al’ummar Fagge Gwamna Kano Alhaji Abba Kabir Yusif, gatan CRC ya ba mu lambar yabo da kofin na cewa Fagge ce ta ɗaya a ƙoƙarin akin CRC.

By ukarofi