Kotu ta cire Abure tare da tabbatar da Nenadi a matsayin shugabar jam’iyyar LP

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Kotun tarayya a Abuja ta tsige Julius Abure daga mukamin Shugaban Jam’iyyar Labour Party (LP), tare da umartar hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) ta amince da kwamitin riƙon kwarya na jam’iyyar karkashin jagorancin Sanata Esther Nenadi Usman.

Mai Shari’a Peter Lifu ya yanke hukuncin ne bisa dogaro da hukuncin kotun koli na ranar 4 ga Afrilu, 2025, wanda ya tabbatar da cewa wa’adin mulkin Abure ya ƙare, tare da ayyana Sanata Nenadi Usman a matsayin sahihiyar shugabar LP har zuwa lokacin da jam’iyyar za ta gudanar da babban taron ƙasa.

Kotun ta ƙi amincewa da hujjar Abure cewa batun na cikin gida ne na jam’iyya, tana mai cewa kafa Kwamitin Riƙon Kwarya ya zama dole sakamakon umarnin kotun koli.

Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da Sanata Nenadi Usman ta shigar, inda aka ambaci Abure da Kungiyar Kwadago ta Nijeriya (NLC) a matsayin waɗanda ake ƙara.

Idan za a iya tunawa cewa rikicin shugabanci ya haddasa tsige Abure daga mukami ta hannun Kwamitin Zartarwa na ƙasa (NEC) na jam’iyyar, wanda daga bisani ya kafa kwamitin riƙon kwarya mai mambobi 29, bayan taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Umuahia, Jihar Abia, ƙarƙashin jagorancin Mista Peter Obi.

Kotun ƙoli ta riga ta soke hukuncin da kotunan ƙasa suka yanke a baya, tare da jaddada cewa jam’iyyun siyasa su rika bin dokokinsu, kuma shugabannin da wa’adinsu ya ƙare su bar mukamansu.

By ukarofi