Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Sakataren Jam’iyyar APC na ƙasa, Felix Morka, ya ce, “idan lokaci ya yi”, jam’iyyar za ta yi magana a kan batun tsige gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, da mataimakiyarsa, Ngọzi Odu.
Mista Morka ya bayyana haka ne a ranar Litinin da daddare a yayin da yake hira da gidan talabijin na TɓC News.
Mai magana da yawun jam’iyyar APC ya jadda cewa jamiyyar tana sane da rikicin siyasar da ake fama da ita a jihar Ribas.
“Duk da ba na son na ce komai a kan rikicin siyasar Ribas, ba hakan yana nufin APC ba ta sane da rikicin da ke faruwa ba.”
“Mu jam’iyyar siyasa ce kuma mai sanin yakamata. Aikinmu shi ne kula da jam’iyyar da sanin yakamata. Idan lokaci ya yi, za mu faɗi matsayinmu da matakin da za mu ɗauka kan rikicin siyasar Ribas. Ina tabbatar muku cewa zan zo nan na faɗa muku matakin da muka ɗauka,” ya bayyana.
“Sai dai kasan akwai hanyoyin da ya kamata a bi domin ya zama a ƙarshe an yi aiki mai kyau.”
Mai magana da yawun jam’iyyar ya yi watsi da rabuwatar gida biyu a jihar Ribas.
Rahotanni sun nuna cewa akwai tsagin APC a jihar a ƙarƙashin Emeka Beke wacce ta fitar da jawabi tana neman babban jojin jihar, Simeon Chibuzor-Amadi da ya yi biyayya ga umarnin kotu domin dakatar da tsige gwamna Fubara da mataimakiyarsa.
ɗaya tsagin APC a ƙarƙashin Darlington Nwauju ya fitar da jawabi game da buƙatar majalisar dokokin jihar ga babban jojin jihar, a ranar 16 ga watan Janairu, kan ya binciki zargin da ake yi wa Fubara da mataimakiyarsa na aikata laifi.
Sai dai a yayin hirar da Morka ya yi da TVC, ya yi watsi da jawabin tsagin APC na Mista Bekee a jihar Ribas.
Mai magana da yawun APC ya ce, Mista Nwauju ba shi da hurumin yin magana a madadin APC a Ribas kuma ba shi da hurumin fitar da wani jawabi a jihar.
“Ina karanta jawaban da yawo a kan jam’iyyar APC a Ribas a kafafen yaɗa labarai game da shugabannin APC. Ya kamata kafafen yaɗa labarai su nemi ƙarin bayani daga shugabannin APC na ƙasa.”
“Shugabannin jam’iyyar a jihar da suke mambobin kwamitin gudanarwa su ne waɗanda ya kamata su fitar da jawabi.”
“Ba ni da tabbacin wanda ake magana a kai (Mista Nwauju) ɗan jam’iyyarmu ne. Yana cikin tsofaffin shugabanni, amma ba na tunanin yana cikin shugabannin jam’iyyar a jihar,” ya bayyana.
Sakamakon rikicin da jam’iyyar ke fama da ita, APC a jihar ta dare gida biyu a yayin da kowanne ɓangare ke iƙirarin shugabancin jam’iyyar.
Tony Okocha shi ne ke jan ragamar tsagi ɗaya a yayin da mista Beke ke jan ragamar ɗaya tsagin mista Nwauju.
Mista Okocha na samun goyon bayan shugabannin APC na ƙasa a yayin da ministan Abuja, Nyesom Wike, ke goyon bayan Beke wadda ke tare da gwamna Fubara wanda a kwanakin baya ya sauya sheƙa a watan Disamba 2025 zuwa APC daga PDP.
A ranar 8 ga Janairu ne aka faras shirin tsige gwamnan Ribas a karo na uku tun bayan zaman sa gwamnan jihar a shekarar 2023 a yayin da dangantakarsa da Wike ta ƙara yin tsami.
Yunƙurin sauke shi na zuwa ne bayan da Wike ya tuhumi Fubara da saɓa wa yarjejeniyar zaman lafiya shugaba Tinibu ya jagoranci kafa ta.
Nan da nan tsagin APC na Bekee ta yi watsi da shirin tsige Fubara, tana mai kira da wararware rikicin.
Wannan kira ya yi tasiri bayan da ‘yan majalisa 4 suka janye da amincewa da sauke Fubara daga muƙaminsa.
Sai dai majalisar ta gaza sake zaman da ta tsara yi a ranar 15 ga Janairu saboda zargin akwai yuwuwar ‘yan majalisar za su iya kauracewa yunƙurin tsige gwamnan.
A ranar 16 ga Janairu, ‘yan majalisar sun sanar da cewa batun tsige gwamnan na nan ta yadda hatta ‘yan majalisa 4 da a baya suka nuna rashin amincewarsu sun janye tare da nuna goyon bayansu.
Majalisar daga baya ta nemi babban jojin jihar da ya kafa kwamitin binciken gwamnan da mataimakiyarsa.
Bayan wasu awanni kuma sai babbar kotun jihar a Ribas ta fitar da umarni na dakatar da majalisar da babban jojin jihar daga ƙoƙarin tsige Fubara da mataimakiyarsa.
