Kotu ta hana EFCC, ICPC, SSS tsare tsohon Gwamna Yari

Daga BASHIR ISAH

Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta hana hukumar EFCC da takwararta ICPC masu yaƙi da laifuka masu nasaba da almundahana, tsare Sanata Abdul’aziz Yari har zuwa lokacin da kotun za ta saurari ƙarar da ya shigar.

Mai Shari’a Donatus Okorowo ne ya ba da umarnin haka yayin hukuncin da ya yanke kan ƙarar da Michael Aondoaaa ya shigar a madadin Yari.

Kazalika, umarnin kotun ya buƙaci hukumar SSS da ta dakatar da tsare zaɓaɓɓen sanatan.

Alƙali Okorowo ya umarci waɗanda ake ƙara (EFCC, ICPC, SSS) da su gabatar da hujja a zama mai zuwa kan dalilin da ya sa kotu ba za ta saurari buƙatar da ɓangaren Yari ya nema ba.

“An hana waɗanda ake ƙarar tsare mai ƙara har zuwa lokacin zama na gaba don gabatar da hujjoji,” in ji Alƙalin.

Daga nan, Alƙalin ya ɗage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 8 ga Yuni inda kotun za ta saurari hunjjojin da waɗanda ake ƙara za su gabatar mata.

Yari, wanda tsohon Gwamnan Zamfara ne, ya shigar da ƙara mai lamba FHC/ANJ/CS/785/23 ta hannun tawagar lauyoyinsa da suka haɗa da Abdul Kohol wanda Mr Aondoaaa ya jagoranta.

Yari ya shigar da ƙarar ne ran 2 ga Yuni inda ya buƙaci kotu ta hana hukumomin EFCC da ICPC da DSS, tsare shi tare da gabatar wa kotun dalilai 15 kan ta biya masa buƙatarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *